Kotu ta yi watsi da ƙarar dake neman a hana Abba Kabir Yusuf takara

A ranar Litinin din ne wata Babban Kotun Jihar Kano ta yi watsi da karar da Ja’afar Sani Bello, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP ya shigar gabanta, yana neman ta hana Abba Kabir Yusuf yin takara a zaben shekara ta 2019.

A ranar 2 ga watan Oktoban 2018 ne Abba Kabir Yusuf ya ci zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP ta yi a Kano, inda ya samu kuri’a 2,421 inda ya kayar da abokin takarar tasa, Ja’afar Sani Bello wanda ya samu kuri’a 1,258.

Sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon zaben fitar da gwanin, sai Ja’afar Sani Bello ya maka Abba Kabir Yusuf a Babban Kotun Jihar Kano mai lamba 3, yana nema a bayyana shi a matsayin dan takarar gwamnan PDP a Kano, saboda a cewarsa, Abba Kabir Yusuf ya karya Sashi na 8 na Kundin Tsarin Mulkin Jam’iyyar wanda aka yi wa kwaskwarima.

Sashin dai ya yi tanadin cewa, duk wanda ya bar jam’iyyar ta PDP kuma yake so ya kara komawa, dole sai ya rubuta wa sakataren jam’iyyar na mazabarsa, ya sanar da shi niyyarsa ta dawowa jam’iyyar, abinda a cewar Ja’afar Sani Bello, Abba Kabir Yusuf bai yi ba.

Da yake gabatar da hukuncin, Alkalin Kotun, Ahmad Badamasi ya ce an shigar da karar ne bayan cikar wa’adin kwana 14 da doka ta bada dama a shigar da kara, kamar yadda Sashi na 258 (9) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya tanada.

A cewar alkalin, duk wani korafin zabe da yake gaban kotu mai hurumi dole ya zama an shigar da shi cikin kwanaki 14 da doka ta tanada.

“Yayinda a fili yake cewa jam’iyyar siyasa ita ce a sama wajen warware korafe-korafen zabe, amma kotu na iya sa baki don ta ta tabbatar da cewa an yi adalci a tsakanin al’umma.

“A irin wannan yanayi, ana iya kiran kotun ta warware karar don tabbatar da cewa an yi adalci.

“Kamar yadda Sashi na 258 (9) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima ya tanada, duk wata karar zabe dole ne a shigar da ita gaban kotu cikin kwana 14.

“Wannan zaben fitar da gwani da aka gudanar wanda ake kara na uku (PDP) ce ta gudanar da shi tsakanin 1 zuwa 2 ga watan Oktoba inda mai shigar da kara, Ja’afar Sani Bello ya zo na biyu da kuri’a 1,258.

“Amma, duba da wannan al’amari, mai shigar da kara ya shigar da kara ne ranar 16 ga watan Oktoba. Duba da yadda karar take, masu shigar da kara sun yi tunanin cewa sun shigar da karar cikin kwanaki 14 da ake bukata, amma a wajen wannan kotu, an yi watsi da wannan kara saboda sun haura wa’adin da ya kamata su shigar da kararsu”, in ji Mai Shari’a Badamasi.

Bayan yanke hukuncin, lauyan Abba Kabir Yusuf ya bukaci Ja’afar Sani Bello ya ba Abban Naira Miliyan 1, amma lauyan Ja’afar Sani Bello ya roki kotun ba kada ta amsa wannan bukata.
Lauyan Abba ya bayyana farin cikinsa da wannan hukunci, inda ya ce lokaci kuma ya kure wa Ja’afar Sani Bello ballai ya kara shigar da kara.
Ja’afar Sani Bello ya ce zai tuntubi aminansa na siyasa don sanin matakin da zai dauka a gaba.

Ya kara da cewa har yanzu yana nan a jam’iyyar PDP, kuma zai yi aiki tukuru don tabbatar da nasararta a zabubbuka masu zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: