Shugaban mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim ne ya yi wannan jawabi wajen taron ƙungiyar Safinatul Khair Foundation a Kano.

Abubakar ya ce yawan matasan da basu da aikin yi sun ninka masu aikin fiye da tunani, kuma babu hanyar da za a iya magance matsalar illa    samar da hanyoyin dogaro da kai.

Cikin           jawabinsa ya bayyana irin halin      ƙaƙanikayi da ake ciki, wanda ya tabbatar da cewar hanyar da za a iya fita daga ciki ita ce samar da   cibiyoyi daban daban ko ɗaiɗaikun mutane da za su koyawa matasa aikin yi.

Ya ce ilimi na da matuƙar muhimmanci, sai dai ba yadda mutum zai iya kaiwa ga wani mataki illa ya samu wata madogara da za ta zamar masa tsani.

Abubakar ya shawarci shugabannin ƙungiyar da ma sauran jama a baki ɗaya, da su samar da hanya ko cibiya ta koyar da sana a ga matasa, ya ce, ko da a ɗai ɗaikun mutane za su iya yin wannan aiki.

Taron wanda aka yi shi a kan harkar ilimi da     dogaro da kai, ya samu halartar shugaban ƙungiyar da kuma matasa da dama, an yi taron ne a ofishin hizbah da ke Gwale a Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: