Daga Mariya Murtala Ibrahim

Ƴan uwana mata barkanmu da wannan lokaci, da fatan muna cikin ƙoshin lafiya, ya muka ji da yanayin sanyi? Allah ya bamu wucewa lafiya amin.
bisa al ada wannan shafi na duba ne kan yadda za mu kula da jikinmu da ma ƴaƴanmu yadda za mu ƙara shiga zuciyar mazajenmu.

Kamar yadda muka yi magana a kan yanayin sanyi, har ma muka bada wasu hanyoyi da sinadaran da za su taimaka don gujewa lalacewar fatarmu.

A wannan lokaci kuma za mu kawo wasu hanyoyi da za mu bi don inganta lafiyar jikinmu da ta yaranmu har ma da mai gida idan akwai.
Kowa ya sani lokacin sanyi yanay ne da ke taɓa lafiyar jikinmu musamman mata kamar fata, gashi, da ma wasu wurare na musamman waɗanda sanyin ke mana illa har ma ya sa a tsanemu a wasu lokutan.
Ga wani sinadari da za mu haɗa don saka fatarmu yin laushi maimakon bushewa.
Idan za mu kwanta da daddare, ya zamnto munyi wanka sannan mu shafe fatarmu da mai wanda yake da laushi.
Yayin da zamu kwanta kuma, sai mu ɗakko mai mu sake shafawa a tafin ƙafarmu, da kuma na hannumu.
Hakan zai sa idan kin tashi da safe ki ga fatarki ta ƙara laushi saboda rufa da kikayi da bargo, sannan kuma yin hakan zai taimaka wajen ƙara ƙarfin gani a idanunki uwargida.
Sinadari na biyu kuma, bayan kin tashi, kada ki yi wanka da sassafe, don hakan zai iya haifar miki da cutar sanyi wanda mafi yawancin mata suke ɗauke da shi a yanzu, sai ki bari sai rana ta yi ma ana kamar ƙarfe 11 zuwa 12 na rana idan kuma za ki wanka da yamma, sai ki yi da wuri kamar ƙarfe 4 kafin yamma ta yi sosai.
Da fatan za mu jarraba don gujewa kamuwa da cutar sanyi, Insha Allahu za mu kawo muku hanyoyin da ake ɗaukar cututtuka da kuma yadda za mu kiyaye kanmu a fitowa da gaba.