Kwamishinan zaɓe na jihar kano Farfesa R.A Shehu ya bayyana cewa cikin shirin zaɓen 2019 da     hukumar ta shirya, sam sam katin zaɓen da aka yi a mazaɓa ba zai yi aiki a wata mazaɓar ba.

Farfesa Shehu ya ce hukumar zaɓe ta INEC ta        shirya magance duk wata kafa da za a iya yin maguɗi a zaɓe mai zuwa.

“Ko da na urar tantancewa sai da muka samo     wadda ta fi ta baya inganci kuma da ita za a yi aiki, sannan ko da ta samu    matsala za mu ɗage zaɓen mazaɓar da ta samu matsalar zuwa wani   lokaci ba mai tsawo ba.

R.A Shehu wanda shi ne kwamishinan zaɓe na jihar Kano ya koka dangane da yadda wasu mutanen ba su je sun karɓi katin zaɓensu ba, ya ce akwai katin zaɓe na sama mutane sama da dubu 700 a ƙasa.

Sannan ya roƙi al umma da su kasance masu taka tsantsan wajen tabbatar da cewar sun yi duk mai yuwuwa don ganin an yi zaɓe cikinkwanciyar     hankali.

Tuni dai hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar da cewar ta shirya tsaf don ganin ta yi zaɓe nagartacce wanda kowa zai yi na am da shi, duba ga irin       sabbin kayan aiki ingantattu da ta samar don ganin an yi zaɓen ba tare da matsala ba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: