Mu shaƙata
Yadda Naziru ya zama sarkin waƙar sarkin Kano – Matashiya
Yadda aka zaɓo Naziru har ya zama Sarkin waƙa
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya naɗa Naziru Ahmad a matsayin sarkin waƙarsa.
Naziru Ahmad dai ya kasance mawaƙi da a yawa lokuta ke karkata ga masu sarauta.
An zaɓoshi ne ganin yadda ke waƙarsa cikin tsari tareda yanayi na al ada.
Naziru sarkin waƙa na yin waƙoƙi ne waɗanda suka sha bambam da na sauran mawaƙan hausa na zamani.
Yana yiwa kansa kirari da sarkin waƙa ne tun kafin a naɗashi sarkin waƙa, cikin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust ta yi da shi ya bayyana cewa bai san dalilin da ya shigar da shi sana ar waƙa ba, sai dai ya taba mafarkin ya zama mawaƙi tun lokacin yana shekara 7 a duniya.
Cikin tattaunawar ya ce lokacin da ya fara waƙa babu ɗakin waƙa wato STUDIO sai dai ya rera a gaban mutane.
A cikin shekarar 2000 kuwa, sarkin waƙa Naziru ya fara shiga waƙar ka in da na in.
Ko da aka tambayeshi menen dalilin da ya sa ya karkata kan waƙarsa yanayin gargajiya?
Nazir Ahmad ya ce yana yin hakan ne ganin yadda da yawan mawaƙa ke tsayar da kansu kan zamani zalla, kuma yana da kyau a ce mawaƙa na ɗabbaƙa yanayin waƙa irin nazamanin baya kamar shata da ɗan kwairo, sai dai hakan na da wuya ganin yadda rubutawa da rera waƙar ke buƙatar nazari, har ma yake tunanin hakan ne ke hana sauran mawaƙan ɗaukar salonsu.
A cikin tattaunawar an tambayeshi ko shin zargin da ake na yin soyayya da jaruma Hadiza Gabon gaskiya ne?
Ya ce tabbas haka ne, kuma suna ƙaunar junansu amma ba su tsayar da lokacin da za su yi aure ba Allah ne masani sun muƙa al amuransu gareshi.
An naɗa Naziru sarkin waƙar sarkin Kano ne a fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll, a ranar 27 ga watan Disambar da ya gabata.
Manyan jaruman fina finan hausa kamar Ali Nuhu, Sadiƙ Sani Sadiƙ da sauran mawaƙa maza da mata ne suka samu halartar bikin naɗin bayan da aka yi walimar cin abinci a daren ranar har ma mujallar Matashiya ta hango Ado Gwanja a wajen.
Leave a Reply
Mu shaƙata
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
Chiza Dani waƙa ce da ke tashe a kafofin sadarwar zamani wadda matasa maza da mata ke sauraro a kwanakin nan.
Mawaƙi Abdul D. One ya bayyana mana ma’anar kalmar a wata tattaunawa da Mujallar Matashiya.
Ya ce kalmar ya arota ne daga harshen Buzanci yayin da ya yi wata tafiya zuwa jamhuriyar Nijar.
Abdul D. One ya ce tun bayan da ya ga kalmar rubuce a wayar wani abokinsa a Agadez daga wannna lokacin ya dinga bi har sai da ya gano ma’anar waƙar.
A tattaunawar ya tabbatarwa da Mujallar Matashiya cewar bayan gano ma’anar kalmar ashe ta na nufin ‘Daɗina’ wato kalmar masoyi ko masoyiya a harshen Buzanci.
Ya ce kalmar ta yi daidai da sunan soyayya da ake faɗawa masoya mace ko namiji.
A halin yanzu ana shirin ɗaukar bidiyon waƙar da za a fitar da shi ba da daɗewa ba.
Sai dai ya ce babu fim da ake yi a kan waƙar bai sani ba ko nan gaba.
Mawaƙi Abdul D. One wanda waƙoƙinsa ba su fi hamsin ba a cewarsa.
Sai da ya ce a waƙoƙinsa ba wadda ya fi so kamar waƙar Mahaifiya.
Sai wasu kamar Kar Ki Manta Da Ni, Chiza Dani, Ina Sonki da sauransu.
Labarai
Lulu Da Andalu – Sabon Shiri Domin Juya Akalar Kannywood
Yayin da ake ci gaba da samar da hanyoyin nishadantar da masu kallo, kamfanin Blue Sound Multimedia ya haska tallan wasan wkaikwayon da ya samar mai suna Lulu Da Andalu.
Sabon shirin wanda ya tara ƙwararrun jarumai maza da mata, da ma sabbin jarumai da ma’aika masu fasaha domin ganin an ƙirƙiri abubuwa masu ƙayatarwa a cikinsa.
Wanda ya shirya shirin TY Shaba ya bayyana cewar sun shirya shirin ne baya bibiyar tarihi tare da nunw jama’a yadda mutane ke alaƙa da aljanu tun a baya.
Yayin da aka shirya taron nuna tallan shirin wanda aka gayyaci manyan ƴan jarida da ƙararru a ɓangaren, wasu daga cikin waɗand su ka kalla sun bayyana shirin a matsayin wani mataki d zai sauya alƙibilar masana’antar fina-finan Hausa.
Wasu daga cikin waɗanda su ka taka rawa a cikin shirin sun bayyana wa masu kallo rawar da su ka taka a ciki tare da tabbatar da cewar shirin zai kayatar fiye da yadda ake tunani.
Sabon shirin ya samu aikin bayar da umarni daga Kamilu Ɗn Hausa y ace wannan aikin ya ƙunshi sabbin hnyoyi na zamani wanda za su ƙayatar da masu kallo a ckin sa.
Jarumai da masu bayar da umarni da ma masu shirya fina-finai ne su ka halarci ɗakin nuna fina finai na Pltinium a ranar Juma’a domin kallon tallan shirin.
Mu shaƙata
Tsawon shekaru 13 waƙoƙi 100 na rera da bakina – D One
Mawaƙi Abdul D One ya bayyana cewar ya kwashe shekaru goma sha uku yana waƙa, tun lokacin da ya samu asalin sunan D One a makarantar sakadire.
Yayin zantarwarmu da shi ya ce ya fara rubutun waƙa a shakarar 2007, sannan ya fara shiga ɗakin rera waƙa a shekarar 2009.
Ya rera waƙoƙi guda 100 da bakinsa.
Sai dai mawaƙin ya bayyana cewar ba zai iya tuna waƙar da ya fara rerawa da bakinsa ba.
Cikin wata tattaunawar da mujallar Matashiya ta yi da shararren mawaƙin nan da ludayinsa ke kan dawo a masana antar fina finan Hausa wato Abdul D One ya ce waƙar Mahaifiya ya fi ƙauna a rayuwarsa.
Mawaƙin ya bayyana dalilinsa na cewar al’umma sun karɓi waƙar suna ƙaunarta kuma hakane ya sa yake matuƙar son waƙar saboda abinda mutane suke so shi yake ƙauna.
Zantawar tamu bata tsaya iya nan ba har sai da mawaƙin ya bayyana cewar ya yi waƙoƙi da sun haura guda ɗari 100 amma a cikinsu guda biyu rak ya fito a cikin faifan bidiyo.
A karo na biyu Abdul D One ya fito a waƙarsa ta Shalele, bayan waƙarsa ta farko da ya fito cikin faifan bidiyo wato Kece Tawa.
Waƙa ta gaba kuwa itace Zainabu Abu, wadda suka rerata tare da ubangidansa wato Umar M Shareef.
Ana sa ran za su fito tare a cikin faifan bidiyon waƙar wadda itace ta uku wanda D One ke fitowa a faifan bidiyo.
Domin masoyansa su kalla hakan ya sa mawaƙin ke wallafa waƙoƙinsa a shafinsa na youtube Abdul D One.
-
Labarai8 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari
MaxwellBig
March 24, 2019 at 2:58 pm
Hello. I have checked your matashiya.com and i
see you’ve got some duplicate content so probably it is the reason that you don’t rank high in google.
But you can fix this issue fast. There is a tool that
rewrites content like human, just search in google: miftolo’s tools