Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta jaddada cewar har yanzu jam iyyar APC ba ta da ɗan takara a jadawalinsu.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya halarta a Abuja.
Ya ce lokaci ya ƙure wajen gabatar da sunayen ƴantakarar gwamna, a cewar shugaban hukumar sun tsammaci jamiyyar APC amma har yanzu babu wani canji a kan fitar da ƴan takarar.

sai dai Shugaban jam iyyar APC na ƙasa Adams Oshimole ya bayyana cewar tuni suka miƙa sunan ɗan takarar gwamnan Zamfara.

Oshimole wanda ya bayyana hakan, kwanaki kaɗan bayan furucin shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC.
Ya ce sungudanar da zaɓen cikin gida a Zamfara kuma sun miƙa sunan wanda ya lashe zaɓen.
Furucin da hukumar zaɓen ta ƙi yin na am da shi kamar yadda shugaban ya ce ofishinsu da ke jihar bai kaɓi rahoton yin zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna a jihar ba.