Ƴan kannywood sun rabu biyu
Tun bayan wata ziyarar cin abinci da aka kaiwa shugaba Buhari a fadarwa, wanda wasu daga cikin jaruman masana antar suka kai masa tareda jaddada goyon bayansu bisa ƙudirinsa na sake neman takara.
Hakan ya sa wasu daga ciki waɗanda ba a yi tafiya da su ba ƙara ɗaukar azamar marawa ɓangaren siyasa baya, wanda suka tafi Adamawa don nuna goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar.
Al amarin dai ya bar baya da ƙura kasancewar shugabanhukumar tace fina finai na jihar Kano Isma il Afakallahu na cikin waccen tafiya ta marawa shugaba Buhari baya.
Tun tuni dama jaruma Fati Muhammad da ani Musa Danja ke cikin tafiyar Atikun, a wannan karonkuwa ta sun samu ƙaruwa ganin samun rabuwar kai da aka yi a waccen tafiya.
A zaɓen 2015 dai masana antar Kannywood kaso mafi yawa daga ciki sun taka muhimmiyar rawa wajen jawo hankalin masoyansu tare da kira a garesu don zaɓar shugaba Buhari a wancen lokaci, wanda wasu daga ciki suka barranta tafiyar a wannan lokaci.
Ƴan siyasa na yinamfani da magoya bayanmanyan jaruman da nufin kaiwa ga nasararsu, sai dai abin tambayar a nan shi ne, shin hakan ba zai taɓa hasken taurarin da suka maƙale a jikin ƴan siyasa ba?
Kowa ya sani jaruman fim na da farin jinni musamman yadda mutane ke zuba kuɗaɗensu don siyan fina finansu, wasu ma na yin tattaki har inda jaruman suke don saduwa da su.
Ko marawa ɗan siyasa baya zai iya kawo cikas ga jarumai ko masana antar kannywood?
Da yawan mutanen dake sha awa ko kallon fim mutanen ne waɗanda suke da bambancin ra ayi, walau na siyasa ko na aƙida, duk da kasancewar rashin bayyana aƙidar ƴan fim hakanya sa kowanne ɓangare ke ƙaunarsu.
Sai dai a wannan lokaci za a iya cewa tafiyar ta bar baya da ƙura, ba abin mamaki bane samun kuɗi ta hanyar marawa ƴan siyasa baya, haka kuma ba zai zama abin mamaki ba wajen dakushewar ƴan fim ɗin daga ɗokinda jama a ke yi idan sun gansu.
Amma a ɓangaren siyasa mutane na da ra ayi wanda ko a tsakanin ƴan gida ɗaya ake samun saɓani wajen ra ayin siyasa a wasu lokutan.
Babban al amari ne hakan musamman ɓarakar da ke shiga a cikin masana antar ɓoye, ko da a wannan lokaci an samu rabuwar shugabancin tafiyar siyasar kowanne gida, rabuwar da za ta iya shiga cikin shugabancin ƙungiyar ta jiha da ƙasa baki ɗaya.
Mujallar Matashiya ta yi duba kan manyan jarumai da suka yi shura a duniya, wanɗanda ake tunani baiya ƙasarsu ba hatta duniya baki ɗaya na yin na am da cewarsu. Cikin binciken Matashiya ta gano cewa babu guda cikinsu da ya taɓa tsautsayin marawa wani ɓangare na siyasa baya har ma ake zargin hakan ne ya basu damar yin ƙarko a masana antarsu tare da ɗagawar likafarsu har suka yi shuraa duniya.
Burin kowanne jarumi ko jaruma, mawaƙi ko mawaƙiya su shahara yadda duniya za ta yi na am da su.
Ko da a Najeriya a shekarun da suka shuɗe idan muka yi duba cikin mawaƙa za mu ga cewa a cikinsu mawaƙan da suke yiwa shugabanni waƙa sun bambanta, kamar yadda masoyansu ma suka bambanta.
Ba ƙaramin al amari bane dakushewar tauraruwar da ke haskawa musamman ganin yadda wasu ke tunanin ana son ɗorewar zamanninsu a mataki daban daban.