Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Rahoto

Ta yaya za a magance Yajin aikin malaman jami a?

Rahoton da nake ɗauke da shi a wannan wata zanyi Magana kan yanayin yadda ɗalibai kan samu tsaiko a karatunsu sakamakon yajin aiki da ma’aikata kan shiga ko kuma ƙungiyar malaman jami’oi.
Wannan lamari na yajin aiki zamu iya cewa ya zama wajibi akan duk wani ɗalibi cewa bai isa ya fara makaranta ba har ya gama ba tare da an tafi yajin aiki ba, ko dai ta ɓangaren ma’aikata ko kuma ɓangaren ƙungiyar ƴan ƙwadago.
A wani bincike da nayi akan yanayin yadda ɗalibai kan fuskanci Tsaiko wajen kammala karatunsu a dai dai wa’a din da aka ɗibar musu zasu kammala, to muddin jami’ar ko kwalejin ta gwamnati ce to bai isa ya gama a shekarun da aka tsara zai gama ba.
Tafiya yajin aiki a ɗan shekarun da ɗalibi yake karatu yakan kasance sau uku ko huɗu ko ma fiye da haka ya danganta da yadda yanayin yadda ma’aikata suke da buƙata a hannun gwamnati.
Haka zalika a binciken da nayi wasu ɗaliban kan fuskanci matsalar yajin aiki a duk shekara kenan idan ɗalibi yana karatun digiri wanda ake sa ran zai iya gamawa a shekara huɗu to sakamakon yajin aiki zai iya gamawa a shekara biyar ko shida.
Binciken ya kuma yi nazari kan yadda iyaye kan tsara wa ƴaƴansu tsarin karatu tun daga tushe amma da zarar an je matakin jami’a sai abin ya rushe ɗai ɗai ku ne masu sa’a sune suke kammalawa a dai dai lokacinsu shima sai sunyi yajin aiki sai dai ya danganta da yanayin daɗewar da za’a yi.
Lissafin shine ana kai yaro makarantar firamare yana shekara 7 zai kammala a shekara 6 sannan ya shiga sakandare ya kammala a shekara 6, daga bisani ya tafi jami’a inda ake sa ran yayi shekara 4, a lissafin kenan ɗalibi yana kammala karatun digiri da mafi karancin shekaru 23, to amma a wannan lokacin akan samu ɗalibi da zai kammala a shekaru 35 in banda lokacin tafiya bautar ƙasa shine yake rage shekaru.
Bayan matsalar yajin aiki da ɗalibai ke fuskanta a bangaren kammala karatu akan lokaci akwai ƙin fitar da sakamako akan lokaci, wanda kan sa ɗalibi ya rasa sanin makomarshi musamman ɗaliban da suke jarabawar ƙarshe daga nan sai tafiya yi wa ƙasa hidima.
Da kuma rashin cin nasarar jarabawar shiga zan jami’a wato JAMB haka kuma wurin jarabawar tantance ɗalibai shima ana samun rashin sa’a sai kaga yaro ya daɗe yana neman gurbin karatu a jami’o daban daban wanda anan shekaru suke tafiya.
a yanzu haka ƙungiyar malaman jami’oi suna cikin halin yajin aiki wanda sun shafe kusan wata ɗaya suna gudanar da wannan yajin aiki, sai dai har yanzu gwamnati bata biya musu buƙatunsu ba balle su janye, yajin aikin da suke, wannan shi yake kara kawo cikas a karatun ɗalibai.

Idan ba’a manta ba a baya bayan nan ƙungiyar ƙwadago suka shirya tafiya yajin aikin sai baba ta gani, wanda suke kira da a mayar musu da albashin ma’aikata ya zama mafi karanci dubu talatin (30000) a maimakon dubu sha takwas (18,000).
Wanda ƙungiyar wasu gwamnatocin jihohi sun amince wasu kuwa suka ce baza su iya biya ba, wanda daga ƙarshe gwamnatin tarayya ta bawa kwamitin ƙayyade albashi daman duba yuwuwar wannan ƙari, inda kwamitin ya amince da biyan wannan kuɗi hakan ya kawo karshen wannan yajin aiki da aka yi niyar tafiya.
Wannan tsaiko da ɗalibai kan samu a ɓangaren karatunsu yana janyo kyamatar shuwagabanni a zuciyoyinsu, da kuma shiga wani yanayi na ƙunci da takura kasancewar a lokacin da ɗalibi yake zaune a gida ba tare zuwa makaranta ba, ko kuma yana wata sana’a to yakan fada cikin mugayen tunani.
Shin ya ɗalibi yake ji a lokacin da aka ce an tafi yajin aiki, tambayar da nayi wa wani ɗalibi kenan dake jami’ar Tarayya dake Dutse wanda muka sakaye sunanshi inda yace ai shi wannan yajin aiki kamar shi aka cuta ma kasancewar ya gama karatu har yayi jarabawar ƙarshe amma kuma ya samu matsala wannan dalili yasa yanzu sai yayi zaman shekara guda a gida kafin ya tafi hidimar ƙasa to ire iren mu muna da yawa a cewar ɗalibin.

Su kuwa ƙungiyoyin ma’aikatu daban daban da na ƙwadago sun bayyana cewa babu wani mataki da ma’aikata zasu ɗauka don gwamnati ta sauraresu akan bukatunsu bai wuce su shiga yajin aiki ba, kamar yadda shugaban ƙwadago reshen jihar kano kwamared Kabiru Ado minjibir ya bayyana ga manema labarai.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: