Tare da Maryam Muhammad Ibrahim
Uwargida barkamu da warhaka sannumu da ƙara kasancewa ta cikin shirin girke girke mujallar matashiya
A yau za mu kawowa uwargida da amarya yadda za ku sarrafa miyar kuka,
Kayan haɗin sune kamar haka
Kuka
Daddawa
Wake
Kayan kamshi
Albasa
Attaruhu
Mai
Kifi
Nama
Mai sa ɗanɗano
Da farko za ku samu wake da daddawa Ku, dakasu, sai Ku   jajaga albasa da attaruhu sai ku, dura tukunyar Ku sannan, Ku zuba mai yayi zafi sai Ku zuba wannan kayan da Kukada, kasu acikin mai sai Ku razana su    sannan, Ku tsai da sauwa dai dai yadda kuke da bukatar     yawan miyarku, sai ki wanke naman  ki zuba a ruwan miyar sai ki sa mai dadano da kayan kamshi a,ciki sai ki rufe          yaddahu sosai ya soma konewa, daman kin gyara kifi  kincire kayar jikin sa    idan ruwan miyar ki ya soma konewa sai ki zuba kifin sannan ki dauko kuka ki kadata  ammafa da kauri zaki kada bakamar an dauraye tukunya ba sai ki sauke.        Wannan miyar kukar tana da matukar amfani a jikin Dan     Adam don tana ƙara lafiya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: