
Ɗan takarar majalisar tarayya a ƙaramar hukumar Nassarawa Muhammadu Aminu Adamu Abba Boss ya yi iƙirarin bijirewa madugun kwankwasiyyar na ƙasa rabi u Kwankwaso bisa ƙin musu adalci da yayi a zaɓen fidda gwani kamar yadda ya faɗa.

Tuni dai Abba Boss ya yi adabo da jar hula, wadda ke nuni da mubaya a ga jagoransu a ƙaramar hukumar Nassarawa Bala Gwagwarwa.

Cikin shirin Abokin Tafiya da ƴan siyasar gidansa kan ɗauki nauyin duk wata sannan a wallafa a cikin mujallar da ke fita duk farkon wata, Abba Boss ya bayyana irin takaicinsa bisa yadda wasu mutane ke nuna cewar kwankwaso ne silar arziƙinsa amma ya butulce masa.
A bayaninsa ya bayyana yadda ya yi aiki da ƙasashen duniya, tare da manyan attajiran ƙasar nan, Abba Boss ya ce lokacin da yake da arziƙi kwankwaso bai san menene neman kuɗi ba.
“na fi shekara 4 rabon da buƙata ta kuɗi ta sameni na rasa yadda zanyi” inji Boss.
Da muka tambayeshi ko ya matsayin ƙudirinsa na tallafawa al ummar yankinsa wanda hakan ne ya kaishi ga takara, ya ce, duk da cewa an musu ƙarfa ƙarfa wajen ƙin yin zaɓe, ammma hakan ba zai sa su karaya waje cigaba da ɗorawa da ayyukan alheri da suka ƙudira ba tun farko.
“tun tuni ma kwankwaso ya ganni ina cikin hidimomina, kuma ya sameni ina tallafawa al umma da ginin ajizuwa, wanda hakan ne ya sa aka danƙamin amanar koyawa mata kiwon kaji.
Bayan nan ko a yankina ina ƙoƙarin ganin na taimaki matasa da marayu da ma waɗanda suke da himma don tsayawa da ƙafarsu, baya ga ciyarwa da muke yi akai a kain, hakan ya sa za mu kafa gidauniya don taffawa irin waɗannan mutane tare da neman mutanen da suke a shirye don bada tallafi ga mabuƙata na yadda za mu kawowa al ummarmu cigaba” cewar Boss.
Batun siyaa kuwa da muka tambayeshi cewa ko ya jingine jar hula da tsarin kwankwa siyya? Sai ya ce a da, kwankwasiyya tana cikin tsari, amma yanzu kwankwaso ya sauketa daga layi, kuma dole ne ya faɗa masa gaskiya har sai lokacin da ya farga ya gyara domin hakan ba zai sa su karaya ba tunda dai su ne mutanen da suke da kishinsa ba wanɗanda za su kaishi su baro ba.
A halin da ake ciki dai a yanzu tuni aka hango jagora kwankwasiyyar na ƙaramar hukumar Nassarawa Bala gwagwarwa tare da wasu mutane na jikin madugun a fadar shugaban ƙasa wanda ake zargin cikin jam iyyar suka koma.
Shirin Abokin tafiya, muna sakashi ne a shafinmu na Youtube, za ku iya kallonsa a duk nda kuke a faɗin Duniya, sunan tashar
Ya ce duk da dumbin magoya bayansa za su iya taimakon wata jam iyyar alhalin yana nan daram a kwankwaiyya, a cewar dan siyasar a ƙaramar hukumarsa Bala Gwagwarwa shi ne jagoransu kuma ko a yau ya umarcesu su fita daga PDP kwankwasiyya za su barta.
Hakan dai ta fara faruwa da ƙusoshi a kwankwasiyyar ne tun bayan zaɓen fidda gwani na jam iyyar da ya gudana, wanda ya ce ba zaɓe aka yi ba naɗawa aka yi.
Cikin jawabin nasa, Abba Boss ya ce ko da gwamnan Kano Ganduje za su iya taimakonsa a siyasar duk da saɓanin da ke tsakaninsu da mai gidan nasu kwankwaso amma shi ma ya taka rawa a zamanin mulkinsa.
MUJALLAR MATASHIYA.