Masu biye da mu a wannan shafi mai albarka Assalamu alaikum warahmatullah. Barkan mu da saduwa a wannan lokaci da muke adabo da Wannan shekara ta 2018.

Muna rok’on Allah yasa mu shiga sabuwar shekara ta 2019 lafiya ya sada mu da alkhairan da take tafe da su ya tsare mu sharrinta.

Duk Wanda ya nazarci tarihin ‘Yan siyasa a K’asar nan tun daga  jumhuriya ta farko zamanin su firimiyan Jihar Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da      Firaminstan farko Sir Abubakar Tafawa B’alewa zuwa yau, zai fahimci cewa a fad’in Nigeria ba a tab’a samun d’an siyasar da ya samu tsarkakakkiyar soyayyar al’umma da yardarsu kamar shugaba          Muhammad Buhari ba. Sakamakon kyakkyawan zaton da suke masa na cewa shine maganin matsalolin da suke addabar su, yasa suke masa lak’ani da mai gaskiya. Da yawan Arewatawa wadanda yawancin su Musulmai ne Suna kallonsa a matsayin wani waliyyi da Allah ya yiwa ilhamar yadda zai tsare hakk’ok’insu da martabarsu daga danniya da wariyar da suke           fuskanta daga abokan zamansu. Amma a lokaci k’ank’ani sai ga soyayyar da al’umma kewa Shugaba Buhari tana raguwa, k’arfin yak’inin da suke da shi a kan zai iya kare hakk’ok’insu a matsayinsa na d’ansu ya yi sanyi. Abin tambaya anan menene dalili? kafin mu kai ga sanin dalilin akwai buqatar mu    waiwayi taskar tarihi, domin mai karatu ya fahimci tushen matsalar.

Nigeria yanki ne da yake da yawan k’abilu sama da 260, da Addinai mabambanta. Turawan da sukaiwa yankin mulkin mallaka sun had’e Arewaci da kudanci a shekarar 1914, ta zama  dunk’ulalliyar K’asa. Kundin tsarin mulkin K’asar ya nassanta baiwa  kowanne d’an K’asa  ‘yancin zama da rayuwa a duk inda yake so a fad’in K’asar. Sannan yana da ‘yancin yin Addinin ko Ak’idar  yake so ba tare da tsangwama ba.

Tun bayan juyin mulkin farko da ya faru a ranar 15 ga watan janairu 1967, Wanda ya yi sanadiyar      rasuwa gawrzayen Shugabannin Arewa na farko a tsarin              dimukradiyya.  Tun daga wancan lokacin zaman lafiyar musulmin Arewa ya gigita, domin bak’in burin wad’ansu miyagu da suka nemi    yiwa Nigeria hawan k’awara bai kai ga biyan buk’ata ba, hakan kuma bai sa sun hak’ura ba, sai suka dinga k’irk’iro fitintinun da suka hanawa K’asar zama lafiya.

A wancan lokacin sun fahimci cewa harkar mulkin K’asar nan sai ‘Yan Arewar da hatta turawa sun jinjina musu. Sa’annan sun gane cewa idan dai har za a ci gaba da bin tafarkin dimukradiyya babu yadda za ayi su samu galaba a kan jama’ar Arewar da ke da yawan samun Nasara a dukkan zab’ubb’uka saboda          rinjayensu a K’asar. Sun tabbatar da cewa ba yadda za ayi su ga wallen ‘Yan Arewa a siyasance idan ba    amfani suka yi da bambancin Addini da k’abilanci ba don rarraba kawunan ‘ya’yanta.

Hakan ne ya janyo k’yank’yasar miyagun mutane irin su Rabaran Bak’o, Wanda munanan lafuzansa a kan Annabi Muhammad (SAW) da Alk’ur’ani ya janyo  Kafancan ta   Kaduna a 1987. Shekara biyu bayan hakan aka sake kwatawa a Zangon kataf. Nan ma akaiwa Musulmai kisan kiyashi.

Dukkan gwamnatin da aka kafa a K’asar nan, walau ta soja ce ko ta farar hula, sai da                                makirce-makircensu ya hana mata zama lafiya. Dangane da haka ne Nigeria ta fad’a  cikin mawuyacin hali yanzu sama da Wanda ta samu kanta a ciki a tsawon watanni 30 da akai  ana yak’in basasa da k’abilar Ibo suka haddasa. Abubuwa sun ci gaba da gudana cikin rashin jin dadi, sakamakon rikicin Addini da ke kunnuwa nan da can a yankin Arewacin Nigeria, Wanda a           kodayuashe yake k’arewa a kan Musulmai.

Sannan hakan ya zama abin nan da ake cewa a dake ka a hana ka kuka.

Kwatsam sai aka wayi gari da    musibar Boko haram, a Arewacin Nigeria wacce ta yi sandiyyar lak’ume dubun nan rayukan      al’umma.  Ana  cikin tsakiyar       Wannan musiba ne, Allah ya kawo shugaba Muhammad Buhari kan kujerar mulkin K’asar nan. Wanda dole a jinjinawa namijin k’ok’arin da ya yi wajen magance Wannan matsala in ka cire abinda ba a rasa ba.

To daga wannan waiwayen da muka yi a cikin taskar tarihi za mu fahimci daga nan masomin rikicin satar shanu da garkuwa da mutane da ake fama da su a Wannan lokacin ya fara. gwanayen magana na cewa ma-so-abinka ya fika dabara. Wannan batu haka yake, domin kuwa       miyagun mutanan da suka hana jama’ar K’asar nan sakat,               musamman musulman Arewacin Nigeria. Sun sake dabarun ganin cewa sun hana su walawa. A yanzu haka mutanen jihohin Sakkwato, zamfara, kebbi da kuma wani b’ngare na  Kaduna Suna cikin       d’ar- d’ar ne saboda yadda miyagu suke kukkutsawa gidajen mutane Suna yiwa mata fyade sannan su yi  awon gaba da su domin neman kud’in fansa. A watannin nan abin ya kuma tsamari a d’aukacin Jihar Zamfara, Wanda takai ga mayar dubun nan mata zawarawa, ta         mayarda dubun nan yara marayu. Duk soyayyar d’a da uwa amma tana ji tana gani wasu tsinannu za su raba ta da d’anta su raba ta mijinta su raba ta da duk ahalinta su yi gaba da ita.

Kwanaki kad’an kenan al’ummar k’aramar hukumar tsafe suka fito domin yin zanzagar lumana a kan halin ko in kula da gwamnatin jiha da ta tarayya suke nunawa a kan lamarin, amma aka k’i sauraran kokensu. Sai ma tukwaici da suka samu na k’ara salwantar da rayuka da raunata wasunsu. Wannan fa k’ark’ashin gwamnatin da suke ganin ta su ce domin ta d’an yankin su ce. Mai girma shugaban k’asa  menene laifinsu?  Dan kawai   Musulmai ne? Jira kake sai an k’arar da rayukansu ne? Ko kuwa Dan sun ba ka kulliyyar soyayyarsu da yardarsu?? A matsayin ka na tsohon soja da kake da masaniya a kan harkar tsaro, me ya hana a ka karb’e Jihar daga hannun gwamnan Jihar kasa dokar ta b’aci?

Kamar yadda obasanjo ya yi a      lokacin rikicin Jos.

Leave a Reply

%d bloggers like this: