Jaruma Rahama Sadau ta yi bikin kammala karatun Digiri wanda ta yi a jami’ar Eastern Mediterranean ,da ke ƙasar Cyprus.
Jarumar wadda ta ɗauki hotuna zafafa ta kuma saka a shafinta na Instgram ta bayyana farin cikinta bayan bikin kammala karatun nata.
Rahama Sadau yar shekaru 25 a duniya ta kasance mai fitowa a fina-finan Hausa da ma na kudancin ƙasar Najeriya.