Wani Lauya a jihar Kano Barista Ma’aruf Yakasai ya bayyana cewar ba dai-dai bane ƙauracewa kotu don sauke alƙalin-alƙalai ba.

yayin taron manema labarai da ya yi a Kano ya bayyana ra’ayinsa kan matakin sauke tsohon alƙalin alƙalai na ƙasa.
Ya ce ba wata sanarwa da suka samu a hukumance, sannan kuma babu wani dalili da za su ari rigar da ba tasu ba ba su yafa.

Ma’aruf ya ce dukkanin kotuna sun zauna a Jihar Kano, sannan kuma idan aka ƙi bin tsarin kotu, wato wani lauya ya ƙi zuwa kotu saboda tunanin umarnin ƙin halartar kotun hakan zubar da kimar kotu ne sannan ba zai hana alƙalai cigaba da shari’a ba.

D a yawan gidajen yari na nan cike maƙil da mutane, amma a ce za a ƙi zuwa kotu, duk da cewa wannan al amari bai shafi talaka ba kuma babu dalilin da zai sa a ƙi zaman kotu ko kuma lauyoyi su ƙi halartar kotun a cewar Barista Ma’aruf.

Sannan ya ja hankalin mutane da su cigaba da halartar kotunan don cigaba da shari’ar tare da yin watsi da jita jitan sanarwar da ƙungiyar lauyoyi ta yi na janye jiki daga kotu.

Mujallar Matashiya ta gano cewar da yawan kotuna sun yi shari’a a jihar Kano, sannan lauyoyi da dama sun halarci kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: