Labaran ƙetare
Ingila tayi barazanar ficewa daga ƙungiyar Turai


Daga Ahmad Hysam
Ƙungiyar Tarayyar Turai da ma sauran ƙasashe mambobinta, sun ce lura da ƙuri’ar da ƴan majalisar Birtaniya suka kaɗa da ke yin watsi da yarjejeniyar da Theresa May ta ƙulla da ƙungiyar, akwai yiyuwar za a raba gari tsakanin bangarorin biyu ba tare da wata jituwa ba.
Jagoran tawagar Turai a tattaunawar Michel Barnier da kuma shugaban Hukumar Tarayyar Turan Jean-Claude Juncker, sun ce sakamakon kuri’ar da aka kaɗa a ranar Talata, na ƙara tabbatar da cewa abu ne mai yiyuwa a kai 29 ga watan Maris wa’adi na ƙarshe ba tare da wata yarjejeniya tsakaninsu da Birtaniya ba.
Ministan Kudin Jamus kuwa Olaf Scholz, ya bayyana kayin da Theresa May ta sha cikin zauren majalisar a ranar Talata da cewa babban abin taikaici ne.
To sai dai shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bayar da shawara cewa, kamata ya yi ɓangarorin biyu su fara tattaunawa domin tsawaita wa’adin ficewar kasar ta Birtaniya, yana mai cewa ko shakka babu, yan Birtaniya ba za su yi fatan ganin jiragensu sun daina tashi daga Turai ba, tare da hana su yin cinakayyar da za ta kai kashi 70% da ƴan uwansu na yankin Turai ba.
A nasa ɓangare kuwa Firaiministan Austria Sebastian Kurz cewa ya yi, sam ba za a zauna da Birtaniya don sake bitar yarjejeniyar da aka kulla a baya ba, yayin da takwaransa na Spain Pedro Sanchez ya ce, isa wancan lokaci ba tare da an cimma wata matsaya ba, lamari ne da zai shafi kowanne daga cikin bangarorin biyu.





Labaran ƙetare
Saudiyya Ta Haramta Auren Ƴan Ƙasa Da Shekaru 18


Ma’aikatar shari’a a ƙasar Saudiyya ta saka dokar hana aurar da mutanen da suke ƙasa da shekaru goma sha takwas.

Ministan shari’a kuma shugaban majalisar alƙalai a ƙasar Sheikh Walid Al-Samaani shi ya sanar da hakan bayan da ƙasar ta amince a kan dokar.
An aike da umarnin hakan ga dukkan kotu a ƙasar don tabbatar da dokar.

Tun tuni ake ta sukar lamarin auren ƙasa da shekaru 18 wanda ake ganin na kawo cikas ga lafiya da rayuwar ƴaƴa mata.



Labaran ƙetare
Joy Biden ya doke Trump a zaɓen shugaban kasar Amurka


Ɗan takarar shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya lashe zaɓen shugabancin ƙasar da ƙuri u 273, yayinda mai bi masa a ƙuri a Donald Trump ya samu ƙuri u 214.

Sakamakon ya kammala bayan ƙidaya ƙuri ar jihar Pennsylvania, jihar da ɗan Donald Trump ke zargin an juyar da adadin masu zaɓarsa.
Joe Biden shi ya yi takarar ƙarƙashin jam iyyar Democrat yayin da Donald Trump ke takara ƙarƙashin Republican.




Labaran ƙetare
Masu Korona ƙasa da mutane dubu goma ne kaɗai suka rage a Saudiyya


Aƙalla mutane 340,089 ne suka kamu da cutar Korona a ƙasar saudiyya bayan samun sabbin mutane 474 da suka kamu da cutar a jiya talata.

Hukumar lafiya a ƙasar ta wallafa cewar an samu mutane 19 da cutar ta hallaka a jiya.
Cikin sanarwar da hukumar ta fitar ta ce mutane 326,339 ne suka warke daga cutar a fadin ƙasar sai mutane 5,087 da cutar ta yi ajali a faɗin ƙasar baki ɗaya.

A yanzxu haka dai mutane 8,663 ne ke ɗauke da cutar sai mutane 839 da suke cikin mawuyacin hali a sanadiyyar kamuwa da cutar.

Tuni aka fara komawa harkoki a ƙasar sakamakon shawo kan annobar cutar wadda ta yi sanadiyyar rufe wuraren ibada, kasuwanni, da wuraren wasanni.


-
Labarai1 week ago
Da Ɗumi-Ɗumi A Na zargin Bam Ya Tashi a Unguwar Sabon Gari A Kano Yanzu
-
Labaran jiha1 week ago
Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane Shida Sun Tafi Da Sarkin Garin Ƙarfi Dake Jihar Kano
-
Labarai2 weeks ago
ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi
-
Labarai2 weeks ago
INEC Ta Sanar Da Ranar Rufe Yin Rijistar Katin Zaɓe
-
Labarai4 days ago
Za’a Daina Anfani Da Kuɗin Takarda A Najeriya – CBN
-
Labarai6 days ago
Sabuwar Ƙungiyar Ta’addanci Ta Ɓulla A Kaduna
-
Labarai2 weeks ago
An Rufe Makaranta Bayan Ƙone Ɗaliba Da Ranta Bisa Ɓatanci Ga Annabi A Sokoto
-
Labarai2 weeks ago
Jihohi 32 A Najeriya Na Iya Fuskantar Mummunar Ambaliyar Ruwan Sama A Bana