Daga Ahmad Hysam
Ƙungiyar Tarayyar Turai da ma sauran ƙasashe mambobinta, sun ce lura da ƙuri’ar da ƴan majalisar Birtaniya suka kaɗa da ke yin watsi da yarjejeniyar da Theresa May ta ƙulla da ƙungiyar, akwai yiyuwar za a raba gari tsakanin bangarorin biyu ba tare da wata jituwa ba.
Jagoran tawagar Turai a tattaunawar Michel Barnier da kuma shugaban Hukumar Tarayyar Turan Jean-Claude Juncker, sun ce sakamakon kuri’ar da aka kaɗa a ranar Talata, na ƙara tabbatar da cewa abu ne mai yiyuwa a kai 29 ga watan Maris wa’adi na ƙarshe ba tare da wata yarjejeniya tsakaninsu da Birtaniya ba.
Ministan Kudin Jamus kuwa Olaf Scholz, ya bayyana kayin da Theresa May ta sha cikin zauren majalisar a ranar Talata da cewa babban abin taikaici ne.
To sai dai shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bayar da shawara  cewa, kamata ya yi ɓangarorin biyu su fara tattaunawa domin tsawaita wa’adin ficewar kasar ta Birtaniya, yana mai cewa ko shakka babu, yan Birtaniya ba za su yi fatan ganin jiragensu sun daina tashi daga Turai ba, tare da hana su yin cinakayyar da za ta kai kashi 70% da ƴan uwansu na yankin Turai ba.
A nasa ɓangare kuwa Firaiministan Austria Sebastian Kurz cewa ya yi, sam ba za a zauna da Birtaniya don sake bitar yarjejeniyar da aka kulla a baya ba, yayin da takwaransa na Spain Pedro Sanchez ya ce, isa wancan lokaci ba tare da an cimma wata matsaya ba, lamari ne da zai shafi kowanne daga cikin bangarorin biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: