A ranar litinin ne kotun kula da da’ar ma’aikata CCT ta dage zaman sauraren tuhumar babban mai sharia’ar Najeriya, Walter Onnonghen da ya kamata a fara sauraro yau Litini zuwa wani lokaci da ba a fadi ba.
Shugaban kotun CCT Danladi Umar ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne bisa hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke cewa a dakatar da ci gaba da sauraren wannan shari’a a kotun CCT.
Zaman da aka kwashe minti 30 ana yi, kowa ya amince da a dakatar da ci gaba da sauraren wannan kara.
Dakatar da babban Mai shari’a Najeriya, Walter Onnoghen da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a ranar Juma’a ta samu rashin goyon baya da kuma nuna damuwa daga bangaren Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai.
Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar da sanarwar nuna matukar damuwa da yin wannan hukunci wanda Buhari ya dauka a daidai lokacin da za a gudanar da zaben 2019.
Sun fi nuna damuwar ta su ne ganin cewa Buhari ba shi da ikon dakatar da Cif Jojin Tarayya ba tare da aika bukatar yin hakan a gaban Majalisar Dattawa ba.
Sannan kuma sun nuna shakkun cewa su na tababar da yin zabe mai adalci tunda aka cire Onnoghen a daidai kwanaki kadan kafin zaben Shugaban Kasa na 2019.
Shi dai Buhari ya ce ya yi amfani ne da umarnin da Kotun CCT ta bashi cewa ya dakarar da Onnoghen ya nada wani har sai bayan gama shari’ar Onnoghen din.
Amurka ta ce a gaskiya yin haka ya janyo wa Buhari gwasalewa da kuma tababar alkwarin da ya dauka cewa za a yi zabe mai adalci.
Don haka ta shawarce shi da a gaggauta magance wannan matsala gudun kada ta janyo wa Najeriya mumunan rikici.
Ita ma Tarrayar Turai ta nuna rashin jin dadin lokacin da aka yi dakatarwar, wato kwanaki kadan kafin zaben shugaban kasa wanda ta ce ya kawo shakku a kan Buhari.
Turai ta ce za ta zuba ido sosai ta ga yadda gwamnati za ta yi zaben 2019, kuma za ta zuba ido wajen ganin rawar da jami’an tsaro za su taka.
Daga nan sai kungiyar ta yi kira ga jam’iyyun adawa da su bi raddin rigimar kamar yadda doka ta tanada, ba tare da neman tashi-tashina ba.