Ta ya akayi jirgin osinbajo ya faɗo tambayar da
Fadar shugaban ƙasar Najeriya tayi kenan inda ta ce za ta yi ƙwaƙƙwaran bincike kan musabbabin faduwar jirgin mataimakin shugaban ƙasar Prof Yemi Osinbajo a garin Kabba dake jihar Kogi, a lokacin da ya kai ziyarar neman goyon bayan al’ummar yankin kan takarar neman shugabancin kasar da shugaba Muhammadu Buhari ke yi.
A jawabin Babban mataimaki na musamman ga Farfesa Osinbajo, Mr Laoulu Akande yayin ganawarsa da manema labarai kan batun, ya ce tabbas za a gudanar da kwakkwaran bincike don sanin abin da ya haddasa faduwar jirgin.
Laolu Akande ya ce Osinbajo da tawagarsa na cikin ƙoshin lafiya babu wanda ya samu rauni a haɗarin,bayan haɗarin nan take ya ci gaba da ziyarsa ta neman haɗin kan al’ummar Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: