Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai Labarin wasanni

An gano ɓurɓushin gangar jikin Ɗan wasan da ya ɓace a jirgi

Rahotannin da muke samu daga kasar Ingila na cewa jami’an binciken cikin ruwa na gaggawa sun gano gangar jikin da ba a tantance ko wane ne ba tsakanin Emiliano Sala da Ibbotson kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A daren ranar Lahadi ne dai jami’an suka bayyana cewa sun gano wani ɓangare na jikin jirgin wanda ya ɓata da mutanen guda biyu akan hanyarsu ta zuwa birnin Cardiff na kasar Wales a ranar 22 ga watan Janairun daya gabata.
Masu binciken sun bayyana cewa sun gano gangar jiki ajikin wani ɓangare na jirgin da yake ɗauke da mutanen guda biyu kuma zasu tsananta bincike domin gano ragowar sassan mutanen guda biyu.
Jami’an dake gudanar da binciken sunyi alƙawarin tuntuɓar ƴan uwan mutanen guda biyu da suka ɓata don su tantance mutanen da bawa ƴan uwansa.

Emiliano Sala dai , ɗan asalin ƙasar Ajantina ne ya hau jirgi ne domin komawa sabuwar ƙungiyarsa ta Cardiff City dake buga gasar firimiyar Ingila bayan da ƙungiyar ta siyeshi daga kungiyar Nantes ta kasar Faransa kuma tun ranar da suka bar filin jirgi aka nemesu aka rasa, shi da Ibbotson matuƙin jirgin.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: