Wani babban malamin addinin musulunci a Jami ar Ahmadu Bello da ke zariya Dakta Jamilu Zarewa ya yi wannan bayani ne a shafinsa Na Facebook Inda ya wallafa tambayar ko ya halatta Matar aure ta yi aikin Jarida?

Sai dai ya bayyana dalilansa Wanda ya ce yana saga cikin abin da ka iya kawo haramcin hakan sanadin cudanya da maza, Wanda ya sabawa Shari a.

A cewar Dakta Zarewa, matukar za a kaucewa dukkan wani al’amari da zai haifar da kokwanto cikin aiki, babu laifi amma abu ne mai matukar wahala a iya samar da yanayin da mata za su gudanar da aikin jarida bisa halaccin addinin musulunci.
