Connect with us

Ana yi da kai

SAI MA MUN JE RANO

Published

on

Wani mutum ne dan Najeriya yabar kasarsa ya tafi Amerika domin yin aiki tsawon shekara da shekaru har yayi aure a can yayi yaya amma bai dawo Najeriya ba, abinka da Amerika kome yaro yama baza ka dake shi ba saboda dokar yancin Dan Adam, yaransa sun fara girma kuma sun dame shi da rashin ji shi kuma bai iya dukansu ba saboda doka, wata rana sai ya shirya dabara, ya cewa yaran za suzo Najeriya ganin gida kuma suga kakanninsu, yara sai murna, suka shirya suka hawo zuwa Najeriya koda saukarsu a iyafot(airport) sai aka dauke wuta, can sai sauro, yara sai suka fara kuka,babansu yace baku fara kuka bama sai munje Rano.

Click to comment

Leave a Reply

Ana yi da kai

An Gano Ƙungiyoyin Addini Uku Da Ke Goyon Bayan Ayyukan Ƴan Bindiga A Najeriya

Published

on

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara a kan al’amuran tsaro a Najeriya Babagana Munguno ya fallasa wasu ƙungiyoyin addini guda uku da ke goyon bayan ayyukan yan bindiga a Najeriya.

Babagana Munguno ya bayyana haka ne a wani taron malamai da limamai da ya gudana a Abuja.

Ƙungiyoyin su ne Jama’atr Nasr Al-islam Wal Muslimina (JNIM) da Islamic And Muslim Support Group (IMSG) sannan Islamic State in Greater Sahara (ISGS).

Ya ce daga cikin su akwai wadanda ke iza wutar rikici a kasashe Mali, Niger da Burina Faso.

Munguno ya buƙaci limamai da masu da’awa da su mayar da hankali wajen ci gaba da wa’azi a kan muhimmancin zaman lafiya tare da bai wa jami’an tsro haɗin kan da ya dace.

Continue Reading

Ana yi da kai

Ko Za A Kashe Ƴaƴa Na Idan Aka Sace Su Ba Zan Biya Kuɗin Fansa Ba – El’rufa’i

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna ya sake jaddadda matsayar sa a kan ƙin biyan kudin fansa ga masu satar mutane da su ka addabi jihar Kaduna.

Gwamna Mallam Nasir El’rufa’I ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da gida rediyo Najeriya Kaduna.

Gwamnan ya ce ko da ɗan sa aka kama ba zai biya kuɗin  fansa domin karɓo shi ba.

Malam Nasir El’rufa’I y ace ko da za a kashe ƴaƴan sa idan aka kama su ba zai biya kuɗi domin a karɓo su.

Sannan ya nuna takaicin sa a bisa yadda wasu ke tunanin bai damu da ɗaliban da aka sace ba a jihar sanadin rashin biyan kudin fansa.

Ya ce abin da yake gaban gwamnatin shi ne yadda za a kawo ƙarshen masu satar mutane a jihar baki ɗaya.

Tun a baya gwamnan Kaduna ke iƙirarin ƙin biyan kuɗin fansa ga ƴan bindiga domin a sako mutanen da su ke tsare da su.

Daga ƙarshe ma gwamnatin ta ce za ta hukunta duk wanda ya biya kuɗi ko yake tattauna wa da ƴan bindigan da sunan gwamnatin

Continue Reading

Ana yi da kai

Shirin bayar da ilimi kyauta kuma dole a jihar Kano abin koyi ne ga sauran gwamnoni – Sharhin Jaridar Guardian

Published

on

Fassarar Sharhin (Editorial) Jaridar The Guardian  ta Ranar Juma’a 4 Ga Watan Oktoba, 2019, a Shafi na 16
Mai Fassara Abba Anwar, Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano

A daidai tsakiyar kamfen na kyamar ilimin zamani na boko da wata kungiyar ‘yan ta’adda suke yi a wasu jihohin arewa, sai ga shi jihar Kano, a arewa maso yammacin wannan kasa sun fito da wani tsari na tilasta zuwa makarantar firamare kuma kyauta daga matakin firamare zuwa sakandare.

Hakan ba karamar hobbasa ba ce wacce ta ke neman samun kwaikwayo daga daukacin jihohin arewa. Ya kamata jihohin nan su yi koyi da jihar Kano kan wannan babban al’amari da jihar ta sa a gaba.

Wannan babban al’amari da a ka kaddamar a jihar ta Kano kwanakin baya ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da kwararru a harkar ilimi da manyan masana a harkar ilimi da kungiyoyin kasa-da-kasa na duniya. Cikin wadanda su ka samu halartar wancan bikin kaddamarwa har da Jakadun kasashe kamar su Sa’udiyya, Masar, Amurka, Hadaddiyar Daular Larabawa, da dai sauransu.

Daga cikin wakilan manyan kungiyoyin nan na kasa-da-kasa da akwai daga DFID, UNESCO, USAID da sauran irinsu. Wadanda kowannensu ya nuna cewar a shirye su ke su bayar da goyon bayansu dari bisa dari wajen ganin wannan gagarumin shirin ya samu nasara.

Lokacin bikin, a jawabinsa Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje cewa ya yi “Babban dalilin yin shi wannan taro na ilmantarwa kan wannan manufa ta gwamnatinsa an yi shi ne saboda a na son a tattauna yadda za a samar da hanyoyin aiwatar da wannan manufa ba tare da samun wani tsaiko ba.”

Ya kuma kara tabbatar da cewa shi wannan shiri ya na daga cikin alkawurran da ya yi wa jama’ar jihar ta Kano lokacin da a ke rantsar da shi a dawowarsa kan karagar mulki jiko na biyu. A lokacin ne ya ambata cewar “Wannan gwamnatin ta dauki aniyar aiwatar da shirin bayar da ilimi kyauta kuma dole a matakan firamare da kuma na sakandare.”

Kuma yadda a ka samu halartar manyan Jakadu da kusohin wasu manyan kungiyoyin bayar da tallafi na kasa-da-kasa ya na nuni da cewar wannan gagarumin aikin da gwamna Ganduje ya dauko ba shi kadai ba ne zai fuskanci wannan abu da niyyar magance dukkan matsalolin da ke tattare da shirin.

Kuma lallai jihar Kano karkashin Ganduje ba karamin hobbasa ta yi ba. Wannan kuma shine ya ke nuna daura damara ta gaske da wannan gwamnatin ta yi. Tare da tabbacin cewa an shirya tsaf domin samun nasarar shirin. Duka dai saboda a yi maganin babbar matsalar nan ta mayar da yara makarantu, wadanda suke shekarun shiga makaranta.

Akwai ciwo da takaici idan mu ka kalli alkaluman nan da su ke sanannu cewar  Najeriya ta na da sama da Milyan Da Dubu Dari Biyar wadanda ba sa zuwa makaranta. Mafi munin kuma shine idan a ka yi la’akari da cewar kashi 60 daga cikinsu yara ne mata.

Sa’annan yara Milyan Takwas ne daga cikin wancan kason da su ke daga Arewacin wannan kasa. Tare da cewar kaso mafi yawa daga cikinsu daga jihar Kano su ke. A na maganar sama da Milyan Uku.

Amma fa bincike daga baya ya nuna cewar akwai da yawa daga cikin wadannan Almajirai da suke daga makwabtan kasashen Nijar da Kamaru da Chadi. Saboda domin a samu maganin wannan matsala kacokan ya kamata a ce an samu wani shiri na doka wanda jihohin Arewa za su yi hadin gwuiwa wajen magance wannan matsala.

Kamar dai yadda a kullum gwamna Ganduje ya ke kira da samar da wata hadaddiyar hanya mikakkiya daga jihohin Arewa a hadensu. Wanda a dalilin samar da wata mafita mai dorewa kan harkar Almajirci da magance rashin zuwa makaranta ga yara, gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman na ganin an aiwatar da gudanar da wannan manufa mikakkiya.

Yin hakan kuma zai inganta wani shiri ne na musamman da tsarin nan mai kula da shirin inganta rayuwar yara na Majalisar Dinkin Duniya, wato UNICEF karkashin wani shiri na musamman na ganin an kara inganta samar da ilimi na yaran da a ka mayar zuwa makarantu, wato BESDA.

Tattare da wannan kuma akwai daya shirin na inganta harkar karatun Tsangayu da Islamiyoyi. Wanda a halin da a ke ciki da akwai ire-iren wadannan makarantun sun kai 13,619, wanda su na da yara dalibai sama da Milyan Biyu da Rabi.

Kuma saboda a tafiyar da wannan shiri cikin cin nasara da kulawa ta musamman, hakan ta sa gwamnatin jihar ta Kano ta samar da wata Hukumar Kula da Makarantun Qur’ani da Makarantun Islamiyyah. Hakan ya sa a ka samar da wata hanya mikakkiya kuma ingantacciya wajen kula da ingancin tafiyar da harkokin makarantun da kuma maganin duk wani kalubale da zai iya tasowa.

Kamar yadda rahotannin su ka same mu, an bayyana cewar gwamnatin jihar Kano ta soke biyan duk wasu kudaden makarantun sakandare da da iyayen dalibai su ke biya tun daga watan Satumbar 2019. Haka nan kuma gwamnatin ce yanzu za ta dinga biyan kudaden kula da wadannan makarantu.

Yawan makarantun ya kai 1,180 da dalibai guda 834,366. Kuma yadda lissafin ya ke gwamnati za ta kashe Naira Milyan 200, a duk wata. Wanda hakan shi ya ke nuna cewar a shekara za a kashe Naira Milyan Dubu Biyu da Milyan Dari Hudu (N2.4b).

Shi fa wannan shirin na bayar da ilimi kyauta kuma dole ya na da matukar amfani ga wannan kasa ta mu ta Najeriya. Musamman saboda wasu bayyanannun dalilai. Misali shekaru uku kenan yau cif bayan gabatar da shirin nan na Tabbatuwar  Muradun Karni na 4, har zuwa yanzu babu wata gagarumar nasara da za ka ce an samu wajen rage yawan yaran da suke gararamba kan tituna ba tare da zuwa makaranta ba. Tare da matasa da kuma wadanda su ka dan data.

Kamar dai yadda Cibiyar Kididdiga ta UNESCO ta ambata cewar a sashen Afirka ta Yamma akwai yara da matasa wadanda yawansu ya kai Milyan 258 da kuma Dubu 400 ba sa zuwa makaranta a wajejen karshen shekarar 2018. Rahoton kuma ya kara bayyana cewa a shekarun bayan dai wannan bangaren namu na Afirka shine ya ke dauke da kaso mafi yawa na yaran da da ba sa zuwa makaranta.

Daga cikin yara su Milyan 59 wadanda suke da shekarun zuwa makarantun firamare amma ba sa zuwa, da yawa daga cikinsu sun fito ne daga wannan sashen namu na Afirka. Wasu su kimanin Milyan 32 ko kuma ma a ce sama da rabin wadanda su ke a wannan bangaren namu.

Sannan kasashen kudancin Asia su ke mara mana baya wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta. Sun kai Milyan 13. Sa’annan kuma dai wannan bangaren namu na Afirka mu muke da mafi yawan yaran da a ke danne  musu hakkinsu na zuwa makaranta.  Wanda kaso 19 cikin 100 a ke tauye musu wannan hakkin na su.

Daga nan kuma sai Arewacin Afirka wadanda suke da kaso 9 cikin 100 na irin wadannan yara. Sai kuma Kudancin Asia masu kaso 7 cikin 100. Saboda haka akwai bukata ta gaggawa saboda magance wannan matsala. Sa’annan kuma duk da cewar ilimin firamare kyauta ne kuma dole a wannan kasa ta mu, amma duk da haka kusan yara Milyan 10 da Dubu 500 ba sa zuwa makaranta, kamar yadda hukumar UNICEF ta fada.

Abin lura a nan kuma shine, yawaitar wadannan yara ba zai haifar da da mai ido ba ga cigaban kasa. Saboda haka ba ma amfanin ai ta ranto kudade a na ta faman yin wasu gine-gine. Bayan ba a mayar da hankali wajen gina zukatan jama’ar da za su yi amfani da wadannan abubuwan raya kasar ba. Saboda haka yaran da ba a gina zukatansu ba, su ne kuma wadanda idan sun taso za su yi fancakali da wadannan abubuwan.

Hanya mafi sauki da kyau ga jihohin Arewa wadanda su ka fi wannan matsala shine, a samar da wani yanayi da za a kara shigar da tsarin manhajar karatun Islamiyyu da Tsangayu da yadda tsarin manhajar matakin gwamnatin tarayya yake. Ta haka ne za a gyara tare da tseratar da yanayin karatun Islamiyyu da na Tsangayu yake. Kamar dai yadda jihar Kano ta ke yi a halin yanzu din nan.

Wani kuma abin ban sha’awa shine yadda Kano karkashin Ganduje ta taso haikan domin cimma wannan manufa, ya kasance wata hanya ce ko ‘yar manuniya cewar Kano ta amsa kiran da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na cewar jihohin Arewa su tashi tsaye wajen kara gyara harkar ilimin makarantun Islamiyya.

Hakan kuma ya yi daidai da shirin nan na dokar hakkunan yara mai suna “2003 Child Rights Act” wanda a ka ambaci cewar samar da ilimi ga yaro ya na daga cikin hakkinsa na dan Adam. Saboda haka ya zama wajibi a yabawa gwamnatin jihar Kano saboda wannan babbar hobbasa da su ka yi, na mayar da yara makaranta. Wannan ba karamar dabara ba ce ta gina rayuwar wadannan yaran ta nan gaba.

Ya kuma zama wajibi ga gwamnatin jihar Kano ta fahimci cewar wannan gagarumin shiri na janye yara daga kan titi a hana su gararamba, sannan a sa su ko a mayar da su makarantu abu ne wanda ya fi karfin fada da baki kawai. Musamman ganin yadda matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta ya addabi wannan sashe na mu na Afirka. Kamar kuma yadda masana da kwararru ma su ka fada.

Daga cikin matsalolin da a ke danganta wannan tabarbarewar ilimin yara da su sun hadar da rashin isassu da kuma kwararrun malamai a wadannan makarantu da kuma rashin kayan koyarwa din gami da kyakkyawan yanayin koyarwar.

Haka nan an kara da cewar akwai dalilan kasancewar zaman yaran a irin kauyukan nan na can ciki wadanda harkokin more rayuwa su ke karanci da kuma irin yaran nan da suke da wata tawaya a halittarsu gami da irin yaran da ke wajen sansanin ‘yan gudun hijira haka.

Sannan an gano cewar hatta shi kan sa wajen neman ilimin, muddin ba a neme shi ta yadda ya kamata ba, watakila saboda rashin sanin yadda ya kamata a neme shi kuma mai inganci. Hakan ma ya kan haifar da rashin zuwan yara makaranta.

Hatta ma yadda wasu ke ganin sam sam ma bai kamata a neme shi ba, a na ta sukarsa, misali a nan shine na ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram, wacce ta ke ganin haramci ma na gaba daya kan neman ilimin. Wanda su a na su wajen ma wai shi wannan ilimi ba wani abu ba ne illa harkar shedanci, su a wajen su. Kamar yadda abin ya yi kamari a Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Sannan ma akwai maganar ware wata karamar kabila wajen bayar da shi wannan ilimi. Duk wadannan dalilai ne da suke sa yara su gujewa makaranta. Sannan kamar a Kudu Maso Gabashin Najeriya, su kuma a irin na su tunanin, samun ilimi ba ya cikin abubuwan da suke tallafar rayuwar mutum ya zama mai dogaro da kan sa. A wajen su. Bangarorin kasar dai kowanne akwai irin na sa tunanin kan samar da ilimin zamani.

Akwai tunani mai karfi game da cewar rashin kula da iyakokin kasar nan sosai wajen kula da bakin haure, ya na kara tallafar yanayin nan na haifar da tururuwar yaran da ba sa zuwa makaranta. Kamar dai yadda gwamnan Kano Ganduje ya bayyana cewar mafi yawa daga cikin irin wadannan yaran da ke gararamba ba zuwa makaranta, wasunsu ma daga kasashen ketare shigowa jihar ta Kano.

Saboda haka babban abin lura a nan shine, yin maganin wannan matsala abu ne da yake bukatar tallafin bangarori daban daban. A kan haka ya zama wajibi gwamnatin Ganduje ta samar da wani yanayi da zai kara inganta makarantu tare da samar da kayan aiki na zamani da kyawawan wuraren koyarwa, tare da horaswa kan horaswa na malaman da su ke karantarwa a wadannan makarantu. Tare kuma da dukkan wasu hanyoyin da za su kara inganta koyo da koyarwa.

Sanoda haka mu na kira ga ragowar jihohi da su yi koyi da jihar Kano kan irin wannan hobbasa da jihar ta faro tun daga lokacin da gwamna Ganduje ya kaddamar da wannan kyakkywan shiri na inganta harkar ilimin. Hakan ya na cikin abubuwan da za su kara tallafawa al’umma a nan gaba. Rashin hakan kuma ya na nuni ga wata sangarta da lalacewar al’amurra a nan gaba.

Ya kamata a fahimci cewar akwai wata alaka mai karfin gaske tsakanin ingantaccen ilimi da kuma cigaban tsarin mulkin Dimukuradiyya. Kamar yadda tsohon dan gwagwarmayar nan kuma tsohon shugaban kasar Afirka Ta Kudu, Nelson Mandela ya ce ne “Lafiya da kuma cigaban mulkin Dimukuradiyya ta na samuwa ne ta hanyar samar da al’umma mai ilimi kuma wacce ta ke kan ta a waye.”

Wani abin lura kuma shine, shi fa ilimi wani doki ne da ya ke dauke da ma’anar ainihin karfafa al’umma su san menene ya ke musu ciwo, tare da ba su damar yin zabin da suke so a rayuwarsu ba tare da wani ya zare musu idanu ba.

Bilhasali ma shi ilimi shine ya ke ba al’umma dama su tambayi shugabanninsu ta yaya suke tafiyar da alhakin da a ka dora musu a matsayin shugabannin jama’a. Wanda hakan ya na kara inganta samar da shugabanci da shugabani masu adalci.

Kuma alhakin gwamnatin jihar Kano ne su yi duk mai yiwuwa wajen kara fadakar da iyayen yara, musamman wadanda su ke a karkara da kuma iyayen da su ba su yi karatu ba, cewar ilimim firamare har zuwa sakandire kyauta ne fa. Watakila za ka samu duk abin nan da a ke ta magana a kai, su ba su ma san kyauta ba ne ilimin. Wannan ya na da muhimmanci kwarai da gaske.

Wani kuma babban abin lura a nan shine, saboda gudun kar yaran da ba na nan ba su yi ta tuttudowa jihar Kano saboda ganin wannan garabasa da gwamnatin Ganduje ta kawo, har ma ta kai wadanda a ka yi saboda su su kasa cin gajiyar abin, ya zama dole jami’an shige da fice su kara mikewa tsaye wajen tantance gami da lura da wadanda ke shigo mana, a san daga ina su ke, kuma ina za su je.

Sa’annan kwanaki ko watanni nawa za su yi a wuraren da su ka zo. Saboda haka amfani da katin dan kasa da ragowar hanyoyin yin rajista ta ‘yan kasa ta ke da muhimmancin gaske a wannan tafiyar da ma dukkan al’amurran da ke biyo baya.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: