Tun bayan dogon yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’oi suke gudanarwa na tsawon wata uku.
A jiya dai sun cimma matsaya da gwamnati inda suka amince da cewa yau juma’a 8/2/2019 a matsayin ranar da jami’oi zasu koma aiki.
Zaman dai ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin ministan ayyuka da samar da aikin yi, Chris Ngige,
Wanda kuma Biodun Ogunyemi shine ya wakilci ɓangaren malaman jami’on.
A cewar Biodun sun samu matsaya da zai basu damar komawa kan aiki,
Sai dai kawo yanzu ba’a bayyana cewa gwamnati ta yadda biyawa ƙungiyar dukkanin buƙatun da take so a biya mata kafin janye wannan yajin aiki na tsawon watanni uku.

Leave a Reply

%d bloggers like this: