Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Inec ta ƙara wa adin kaɓar katin zaɓe zuwa litinin, har da asabar da lahadi

Hukumar zabe a Najeriya INEC ta sanar da kara lokacin raba katin zabe bayan wa’adin da ta diba tun da farko ya cika.

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da kara wa’adin rarraba katinan zaben daga yau juma’a zuwa litinin 11 ga watan Fabrairu.

Karin na kwana uku ya kunshi har da ranakun Asabar da Lahadi.

INEC ta ce ta kara wa’adin ne bayan kiranye-kiranyen da ta samu na neman a kara wa’adin raba katinan zaben.

A baya dai hukumar ta ce akwai miliyoyin katunan zaben da masu su ba su je sun karba ba.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP na cikin jam’iyyun siyasa da suka nemi a kara lokacin rarraba katinan zaben.

Akwai daruruwan ‘yan Najeriya da ba su karbi katinsu na zabe ba, kuma hukumar zaben kasar ta ce duk wanda bai karbi katin ba zai yi zabe ba.

Hukumar zaben kasar kuma ta ce bayan wa’adin da ta diba ya kawo karshe a ranar Litinin 11 ga Fabrairu, za ta mika ajiyar katinan zaben da ba karba zuwa Babban Bankin Najeriya har sai an kammala zabe inda za a ci gaba da rijista da kuma raba katinan.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: