Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Siyasa

Zan kyautata kasuwanci da walwalar ƴan jihar kano – Atiku

Miliyoyin mutane ne suka halarci wajen taronAtiku a Kano

Ɗan takarar shuhgabancin ƙasar nan Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya sha alwahin kawar da ƙunci da ya ce ana yi a ƙasar nan muddin ya kai ga matakin da yake nema.

Atiku wanda ya bayyana hakan yayin ziyararsa jihar Kano, ya ce jihar Kano jiha ce ta kasuwanci amma an samu koma bayan hakan a gwamnatin da ke ci, sannan zai tabbatar komai ya koma dai dai yayin da ya kai kan karagar mulkin da yake nema.

Cikin jawabin nasa ya yiwa al’ummar jihar Kano albishirda cewar, zai samawa matasa aikin yi tare da kawar da yunwa wandaa cewarsa al’umma suke ciki a halin yanzu.

Atiku Abubakar ya ziyarci mai martaba sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II inda ya bayyana maƙasudin zuwansa jihar Kano don yaƙinneman zaɓen 2019.

Kwanaki shida kacal suka rage a fafata zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.

Kalli Hotunan ziyarar a yau.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: