Connect with us

Siyasa

Ba’a samun kuɗi a tafiyar Buhari shi ya sa muka barta Adam Zango, Hajara Usman ta koma PDP

Published

on

Cikin wani faifain bidiyo da jarumi Adam Zango ya saka a shafinsa na facebook na bayyana cewar ba a samun kuɗi a tafiyar Gwamnatin Buhari sannan idan sun yi abu ba a yabawa.

Hajara Usman Ta Bi Sahun Adam A. Zango A Tafiyar Atiku

“Da na samu sakon Adam A. Zango, akan cewa duk masoyan sa su zabi Atiku, duk da soyayya ta da Buhari, sai na ji na hakura, domin na biyo Adamu. Adam A. Zango shine mutumin da ya fi kowa halacci da daraja na gaba da shi a kaf cukin kannywood, sannan ya dauke ni tamkar mahaifiyar sa na gaskiya, ni ma a haka nake kallon sa matsayin da na na cikina, Don haka duk inda ya koma ni ma nan zan koma” a cewar Hajara Usman.

Click to comment

Leave a Reply

Siyasa

Ba Iya Yawan Ƙuri’u Ne Ke Sanya Mutum Cin Zaɓe Ba – Alhassan Ado Doguwa

Published

on

Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa cin zabe ba yawan kuri’un da aka kada ba ne kawai, harda bin ka’idoji.

Doguwa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidan Talabijin na Channels TV yayin da yake mayar da martani kan cece-kucen da ake tafkawa dangane da zaben 2023 a jihar Kano.

Ya ce zabuka a tsarin dimokuradiyya irin na Najeriya a kodayaushe suna kan tsari da ka’idoji, kuma tsayawa zabe bisa wadannan ka’idoji ne ke sa a samu ‘yanci da gaskiya.

Ya ce, a gare shi idan aka tambaye shi abin da ke faruwa a Kano, abin da ya saba faruwa ne, Kano ta kasance jiha ce mai ci gaba, mai fafutuka ta fuskar siyasa da akida.

Sannan ya kara da cewa ya kamata mutane su san cewa bawai a zabi mutum shike nuna yaci zabe ba har sai ya cika dukkan sharudan da za su saka ya zama shugaba ga al’umma.

Continue Reading

Siyasa

Jam’iyyar NNPP Ta Gudanar Da Zanga-Zanga A Abuja

Published

on

Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta gabatar da zanga-zangarta zuwa Abuja saboda abin da ta kira da ana neman soke nasararta a zaben 2023.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa shugabannin NNPP sun ce idan har aka karbe gwamnatin Kano daga hannunsu, za a iya haddasa rikici.

A wani jawabi da Ladipo Johnson ya fitar a ranar Laraba, ya yi gargadi cewa wannan rigima za ta iya shafar har sauran kasashe na Afrika.

Shugaban mai binciken kudi ya karanto jawabin da shugaban jam’iyyar NNPP na rikon kwarya, Abba Kawu Ali ya rubuta a ofishin ECOWAS.

NNPP ta kuma yi tattaki zuwa ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniyya da babban ofishin kungiyar EU ta tarayyar Turai a garin Abuja.

Shugabannin na NNPP sun ce daga hukuncin kotun sauraron karar zabe da na daukaka kara, ta fito cewa ana so a zalunci mutanen Kano.

Jawabin Abba Kawu Ali ya ce mafi yawan al’umma sun zabi Abba Kabir Yusuf na NNPP a watan Maris, amma ana shirye-shirye domin a tsige shi. Sai dai jam’iyyar ta ce bazatayi watsi da takardun CTC da aka fitar ba.

 

Continue Reading

Siyasa

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Kori Ƴan Majalisar Dokoki 11 Na Jam’iyyar PDP A Filato

Published

on

Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta soke zaben ‘yan majalisar dokokin Jihar Filato 11 na jam’iyyar PDP, inda ta tabbatar da na jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka samu nasarar.

 

A wani hukunci da kotun ta yanke karkashin jagorancin mai shari’a Oko Abang a ranar Juma’a, sun bayyana cewa kuri’un da dakatattun ‘yan majalisar suka samu ba su halarta ba a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.

 

Alkalin ya bayyana cewa jam’iyyar ta PDP ta sabawa dokar sashe na 177 na kundin mulkin Najeriya na shekarar 1999, kuma hakan ya sanya ba ta cancanci tsayar da ‘yan takarar ba.

 

A hukuncin kotun ta tabbatar da ‘yan takarar na jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka samu nasarar a zaben.

 

Bayan yanke hukuncin a halin yanzu jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a majalisar ta dokokin Jihar ta Filato.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: