Lafiya
Cutar Lasa na cigaba da hallaka al’ummar Najeriya


A wata ƙididdiga da Hukumar da ke kula da cututtuka masu saurin yaɗuwa a Najeriya NCDC ta bayyana cewa tun daga lokacin da aka samu ɓullar cutar Lasa da beraye ke yaɗawa a tsakanin alumma wanda yanzu haka cutar ta hallaka aƙalla mutane 57 a jihohi daban daban na Najeriya.
Hukumar NCDC ta kuma bayyana cewa akwai masu fama da cutar ta Lassa a jihohi 19 na ƙasar, ta kuma tabbatar da gano mutane 275 cikin mutane kimanin 800 da ake kyautata zaton suna ɗauke da cutar., wanda yanzu haka ake basu kulawa ta musamman a cibiyoyin da ke kula da cutar.
Hukumar ta kuma bayyana cewa jihar Edo da Ondo sune suka fi masu yawan ɗauke da wannan cuta, inda a yanzu haka akwai kimanin mutane 40 dake ɗauke da wannan cuta kamar yadda hukumar ta bayyana.
Haka kuma hukumar ta bayyana cewa akwai jami’an kiwon lafiya dake ɗauke da cutar lassa a dai ƙasar ta Najeriya.



Lafiya
Cikin Shekaru Biyu Korona Ta Hallaka Mutane Dubu Uku A Najeriya


Hukumar lura da dakile cutyka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce mutane dubu uku ne su ka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar Korona.

A wata sanarwa da hukumar ta fita, ta ce sama da mutane dubu ɗari biyu aka samu sun kamu da cutar, sai dai fiye da kashi 80 cikin 100 sun warke kuma an sallamesu.
Hukumar ta ce ta samu wasu darrusa na dakile cutuka masu yaɗuwa tun bayan ɓullar annobar Korona da cutar Lassa.

Sai dai a wannan lokaci hukumar ta mayar da hankali ne a kan cutukan Lassa da cutar amai da gudawa wato Kwalara wadda ke ci gaba da yaɗuwa a wasu jihohin Najeriya.

A ranar 27 ga watan Fabrarun da ya gabata ne dai aka cika shekaru biyu cif da ɓullar cutar Korona a Najeriya wadda ta yi sanadiyyar rasa rayuwar mutane dubu uku a faɗin ƙasar.


Lafiya
Ƙasa Da Mutane Miliyan Goma Aka Yi Wa Riga-Kafin Korona A Najeriya


Hukumar lafiya matakin farko a Najeriya ta ce ƙasa da mutane miliyan goma kadai aka yi wa riga-kafin cutar Korona a fadin ƙasar baki ɗaya.

Shugaban hukumar Dr. Faisal Shu’aib ne ya bayyana haka ya ce a ranar 25 ga watan Fabrairun da mu ke ciki alƙaluma sun nuna cewar mutane miliyan 8,145,416 ne su ka karbi riga-kafin cutar.
Wannan na nuni da cewar ba a ɗauki hanyar cimma kson da hukumar lafiya ta duniya ke son kai wa na yi wa adadi sama da 80 cikin ɗari riga-kafin ba.

Dr. Faisal Shu’aib ya ƙara da cewa a ranar 25 ga watan Fabrarun, akwai mutane miliyan 17,646,781 da aka yi wa riga-kafin farko ba a yi musu maimai ba.

Haka zalika a ƙasar, an tabbatar da cewar mutane 254,428 su kamu da cutar yayin da aka gwada mutane 4,317,621 da ake zargi.

Daga cikin mutane sama da miliyan 200 da aka samu su na ɗauke da cutar tuni aka sallami fiye da kashi 70 cikin 100 daga cikinsu bayan an ba su kulawa sannan aka tabbatar sun warke daga cutar.
Faisal Shu’aib ya ce akwai buƙatar sake sabon salo don ganin an cimma kaso na adadin mutanen da ake so a yi wa riga-kafin cutar bisa umarnin hukumar lafiya ta duniya domin kawo ƙarshen cutar a fadin duniya.

Labarai
Najeriya Na zata samar da Maganin Gargajiya na Korona


A yayin da kasashen Turai ke cigaba da yin gwaje-gwaje ingancin maganin Korona da suka hada, Najeriya ma ba a barta a baya ba wajen hadawa da yin nata gwajin magungunan.

Sai dai Hukumar kula da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta bayyana cewa tana yin gwajin magungunan warkar da Korona har guda 40 da masu hada magungunan gargajiya suka mika wa hukumar.
Shugabar hukumar Mojisola Adeyeye ta sanar da haka tana mai cewa ana yin gwajin ingancin magungunan ne saboda tabbatar da ingancin maganin da Alumna zasu yi amfani dashi.

” Haka kuma NAFDAC ta gindaya musu wasu sharudda da dokoki da za su bi wajen hada maganin.

Za dai a fara a yin gwajin ingancin magungunan akan dabbobi a karon farko tukunna.

Mojisola ta gargadi masu maganin kada su kuskura su jaraba wani magani ba tare da hukumar ta bada daman haka ba.

-
Labarai1 week ago
Da Ɗumi-Ɗumi A Na zargin Bam Ya Tashi a Unguwar Sabon Gari A Kano Yanzu
-
Labaran jiha1 week ago
Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane Shida Sun Tafi Da Sarkin Garin Ƙarfi Dake Jihar Kano
-
Labarai2 weeks ago
ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi
-
Labarai2 weeks ago
INEC Ta Sanar Da Ranar Rufe Yin Rijistar Katin Zaɓe
-
Labarai4 days ago
Za’a Daina Anfani Da Kuɗin Takarda A Najeriya – CBN
-
Labarai6 days ago
Sabuwar Ƙungiyar Ta’addanci Ta Ɓulla A Kaduna
-
Labarai2 weeks ago
An Rufe Makaranta Bayan Ƙone Ɗaliba Da Ranta Bisa Ɓatanci Ga Annabi A Sokoto
-
Labarai2 weeks ago
Jihohi 32 A Najeriya Na Iya Fuskantar Mummunar Ambaliyar Ruwan Sama A Bana