Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Siyasa

Jifan Buhari a Ogun rashin ɗa’a ne

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana takaicinta kan yadda aka jefi shugabanninta a gangamin yakin neman zaben shugaba Buhari a jihar Ogun.

Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta ce za ta dauki mataki kan gwamnan jihar Ibikunle Amosun wanda ta zarga da shirya cin mutuncin ga Buhari da kuma shugabanta Adams Oshiomhole.

A ranar Litinin ne wasu suka jefi Adams Oshiomhole a yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke gangamin zabensa a birnin Abeokuta.

An jefi Oshiomhole ne bayan da ya ambaci sunan dan takarar gwamna na APC a jihar, Mista Dapo Abiodun wanda gwamnan jihar ba ya goyon baya, matakin da ya harzuka mutanen da suka halarci gangamin.

APC ta ce ba za ta lamunce wa wannan rashin da’a ba daga duk wani mambanta.

Ta ce za ta yi nazari kan abin da ya faru inda aka kunyata Buhari da shugabanninta kuma za ta dauki mataki akai bayan an kammala zabe.

Lamarin ya kai sai da jam’ian tsaro suka rika kare shugaba Buharir daga masu jifa kafin kammala taron.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: