DAGA SAMA HAR KASA
WANI NE RANAR ZABE AKA BASHI NAIRA 500 AKA CE IDAN YAJE GURIN ZABE YA ZABI JAM’IYYARSU TIN DAGA SAMA HAR KASA, GOGAN NAKA YACE BA MATSALA, DA YAJE ZAI KADA KURI’ARSA SAI YA TUNA DAMA ANCE MASA DAGA SAMA HAR KASA ZAI FARA, DAGA NAN YA FARA DANGWALAWA JAM’IYYU TIN DAGA TA FARKO HAR TA KARSHE, YA GAMA YA FITO, SAI SUKA TAMBAYE SHI, KA DANGWALAMA DAI KO?, SAI YACE AI NA KUSA KARAR DA INKI SABODA DANGWALAWA JAM’IYYU, DAN BA WACCE BAN ZABA BA, SUKA AMMA KAYI MANA ASARA.