Jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce jam’iyyar su za ta yi wa dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ritaya kwata-kwata daga siyasa.

Tinubu y ace zaben shugaban kasa ya wuce a ce kawai zabe ne tsakanin mutane biyu, wato Shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar.
Ya ce zabe ne mai muhimmancin da APC za ta tura Atiku zuwa zaman ritaya daga shiga harkokin siyasa kwata-kwata.

Duk da haka, Tinubu ya ce amma fa ya na so jama’a su sani cewa Atiku abokin sa ne na kusa, tun kafin ya fito takara, har yanzu ma da ya ke takara abokin sa din ne.

Sai ya ci gaba da cewa ya na fatan kuma zai ci gaba da kasancewa abokin sa bayan zaben gobe Asabar idan sun kayar da shi.
“Za mu yi wa Atiku korar yin ritaya daga siyasa don amfanin Najeriya gaba daya, kuma don amfanin shi kan sa Atikun.” Haka Tinubu ya kara bayyanawa a cikin takardar da kakakin yada labaran sa, Tunde Ramanu ya fitar ga manema labarai jiya Alhamis da yamma.
“Mu na so shi ma Peter Obi mu tura shi ritaya tare da Ogan sa, domin su je su zauna su natsu kuma su koyi yadda za su rika tausayin al’umma.
Ya kara da cewa a dukkan tsare-tsare da manufofin Atiku, babu wani abin alheri da ‘yan Najeriya za su amfana.
Da ya juya kan jam’iyyar su ya APC, ya ce a kullum manufofin APC su ne yadda za ta samar wa ‘yan Najeriya ingantacciyar rayuwa a cikin sauki, ba kamar manufofin da ke tattare da jam’iyyar PDP ba.
Ya buga misali da ayyuka irin su ciyar da daliban makaranta da shirin raba kudade na ‘tradermoni’ ga masu karamin karfi ‘yan tireda.
Har ila yau, Tinubu ya kara da cewa “duk da haka APC ba ta ma gamu da ayyukan da ta gudanar ba, shi ya sa ta ke so a kara zabar Buhari domin a kara samun ayyuka nunkin-ba-nunkin fiye da wanda aka samar a wannan shekaru hudu na zangon san a farko.”
Ya ce a zango na biyu Buhari zai kara himma sosai wajen inganta tattalin arzikin kasa.