Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

INEC ta sauya ranakun zaɓen gwamnoni da Shugaban ƙasa

Shugaban hukumar zaɓe na ƙasa INEC farfesa Mahmud ne ya bayyana hakan a yayin zantawa da ƴan jarida, jim kaɗan bayan kammala wani taro da ya gudana a babban birnin tarayya abuja.

Ya ce an ɗage zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisa zuwa ranar asabar 23 ga wannan wata, wato a ƙara mako guda,yayin da za a yi zaɓen gqamnoni a ranar 09 da watan Maris mai kamawa.

Tun tuni dai ake ta zaton hukumar za ta ɗage ranar zaɓen, amma sanarwar ba ta bayyana ba sai bayan da suka kammala taron.

Karanta a nan

 

 

Shugaban INEC na ƙasa farfesa Mahmud ya ce an ɗage zaɓen ne bisa wasu dalilai ciki kuwa har da ƙarancin tsaro, wanda ya ce  sun yi zama na tsanaki kafin tantancewa.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: