Wasu da ake tunanin ƴan boko haram ne sun kashe aƙalla mutane 17 sannan suka tafi da mutum 12 a garin Jere da Gwoza yayin wasu tagwayen hare hare da suka kai.

Wanida abin ya faru a kan idonsa ya shaidawa manema labarai cewa, ƴan bindigar sun kai harin ne kuma yayin da suke tsaka da harbi kan mai uwa da wabi ne wasu suka je suka tashi bama bamai a safiyar Asabar ɗin jiya.
Mutane 15 ne suka jikkata a harin da aka kai.

