Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran ƙasa

Ɗage zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisu bashi da alaƙa da siyasa

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC farfesa mahmoud yakubu ya bayyana dage zaɓen da akayi bashi da alaƙa da siyasa.
Shugaban ya bayyana hakan ne ga manema labarai a lokacin da ake ta raɗeraɗin cewa an shirya wata maƙarƙashiya ne shi yasa aka ɗage zaɓen.

Ya bayyana cewa ɗage zaɓen bashi da alaƙa da ƙarancin kayan aiki ko matsalar tsaro, sai dai bisa dalilin ƙone wasu ofisoshin INEC da akayi a wasu jihohin tare da kayan aiki wannan shine dalilin ɗage zaɓen.

A ɓangare guda kuwa ƴan takarar shugancin ƙasar nan na manyan jam’iyu Muhammad Buhari na APC da Atiku Abubakar Na PDP sun yi Allah wadai da ɗage wannan zaɓe zuwa 23 da wannan wata.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: