Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Siyasa

Za mu cigaba da yaƙin neman zaɓe – Kwankwaso

Cikin wata hira da ya yi da BBC, Kwankwaso ya ce, sanin kowa ne ka’idar dokar hana zabe ita ce sa’oi 24 kafin zabe, to tun da an daga daga na zuwa mako guda da aka kara sai kowa ya je ya ci gaba da yakin neman zabensa.

Ya ce, dama abin da ake gudu ne ya faru.

Sanata Kwankwaso, ya ce ya tabbata ba bu wnada yaji dadin dage zaben nan, fatansa shi ne Allah ya sa kada a sake cewa an daga idan lokacin da aka sanya yazo.

Bayan ɗage zaben shugaban kasa da hukumar zaben Najeriya ta yi a ranar 16 ga watan Fabrairun 2019, wata dambarwa da ta kunno kai ita ce ta batun ci gaba da yakin neman zabe.

A cikin wani jawabi da ya yi, shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce jam’iyyu ba za su ci gaba da yakin neman zabe ba a sauran kwanakin da suka rage kafin sabuwar ranar da aka ware domin yin zaben.

Lamarin da shugaban jam’iyyar APC Adam Oshimhole, ya ce ba za ta sabu ba a lokacin wata hira da manema labarai.

Adams Oshiomhole, ya ce a ka’idar doka shi ne, ana daina yakin neman zabe ne idan ya rage saura sa’oi 24 a yi zabe.

Don haka ya ce, kowa ya san wannan doka, sannna kuma jam’iyyarsu ta APC za ta ci gaba da yakin neman zabe tun da an dage sai wani makon.

Ya ce ‘ Zamu ci gaba da yakin neman zabe saboda mu nuna wa magoya bayanmu cewa kada su yi fushi abin da ya faru ya riga ya faru, don haka su fito su zabi dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyarmu ta APC a ranar zabe’.

A wani bangare kuma, shi ma mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP wato sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba wani ne ya ce a daga zabe ba, to tunda an daga, sai su kyale kowa ya je ya fadi abin da zai fada a yakin neman zabe.

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: