Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran ƙasa

Buhari yayi Allah wadai da hukumar zaɓe kan ɗage zaɓe sannan ya koma Abuja

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin daɗinsa kan abin da hukumar Zaɓe tayi kan ɗage zaɓe.
Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na twita daga bisani ya bayyana wa manema labarai a garin Daura, Buhari ya ce abin takaici ne abin da hukumar tayi kasancewa hukumar INEC ba ta kyautata wa ‘Yan Najeriya ba.
” A kullum hukumar na faɗin cewa ta kammala shirye-shiryen ta zaɓe kawai take jira. Wani abu kuma shine ƙoƙari da gwamnati ta yi na ƙin saka mata baki a harkokin ta sannan kuma gwamnati ta tabbata ta bata duk kuɗaɗen da take buƙata amma sai da ta gaza.
” Abu daya da nake so in jawo hankalin hukumar akai shine, ta tabbata takardun zaɓe da aka riga aka aika jihohi, da wadanda aka rarraba ba su faɗa hannun mutanen da ba nagari ba. Sannan kuma duk abubuwan da ya sa aka samu wannan matsala ba su sake faruwa ba a ranakun da ta tsayar za a yi zaben.
Kuma ya kara da ƙira ga yan Najeriya da su yi hakuri, kada su karaya duk da cewa kowa ya koma jihohinsa na asali domin kaɗa kuri’a da kuma shigowar masu sa’ido da ga ƙasashen waje, hakan bai yi mana daɗi ba ko kaɗan.
Bayan nan Shugaba Buhari yayi kira ga ‘Yan Najeriya da su zauna lafiya da juna sannnan su gujewa yin abin da zai ta da zaune tsaye.
Daga nan sai Buhari ya ya koma Abuja domin cigaba da gudanar da ayyukan da yasa a gaba kafin ranar da aka sa ranar zaɓe.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: