Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran ƙetare

Ƙungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch, ta zargi manyan ƙasashen duniya da kauda kansu kan yadda ake take hakkin Bil Adama

 

sakamakon matsalolin     cikin gidan da suka addabe su.
Ƙungiyar ta sanar da haka ne yayin gabatar da        rahotan ta na wannan     shekara.
Rahotan ƙungiyar na bana yace ƙasar Amurka da    manyan ƙasashen Turai da suka mayar da hakkin Bil Adama a matsayin daya daga cikin manufofin su a ƙasashen waje tun lokacin yakin cacar baka, a yau sun kauda hankali daga kai.
Daraktan ƙungiyar Kenneth Roth, yace matakin            ƙalubalantar take hakkin Bil Adama na raguwa, inda yake komawa kan ƙungiyoyin cikin gida.
Roth yace shugaba Donald Trump na Amurka ya mayar da hankali wajen rungumar shugabannin dake kama karya,       rikicin ficewa daga kungiyar kasashen Turai ya mamaye Birtaniya, yayin da shugaban Faransa            Emmanuel Macron yana kalamai masu daɗi amma kuma baya iya aiwatar da su.
Daraktan yace ita ma       Angela Merkel wadda tayi fice wajen yaƙi da matsalar, yaƙi da masu tsatsauran ra’ayin cikin gida ya ɗauke mata hankali.
Rahotan ya yabawa ƙasashe 57 dake ƙungiyar ƙasashen Musulmi ta IOC da suka tashi tsaye domin        kalubalantar yadda ake cin zarafin yan kabilar    Rohingya a Myanmar, duk da yake kasashen basu ce komai ba kan yadda China ke cin zarafin Musulmi ‘yan kabilar Uighur., dake chana.

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: