Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Mata adon gari

Yadda za ki kaucewa cutar sanyi – Mata kawai

Daga Mariya Murtala           

Ga wadanda suke biye da mu ta cikin wannan shafi mai albarka, a watan da ya gabata mun kwana a dai dai lokacin da za mu kawo hanyoyin da ake kaucewa kamuwa da cutar sanyi, amma a wannan karon za mu duba illar da hakan kan haifarwa mata musamman masu aure.

Sanin kowa ne dai duk macen da ta cika mace     kuma ta san wacece ita, ta kan gyara jikinta               musamman don gudun kamuwa da cutar sanyi    amma akwai illar da hakan kan haifar wanda a lokuta da yawan gaske aure na rabuwa sakamakon rashin gamsuwa da mijin kan yi idan mace na ɗauke da cutar sanyi.

Wasu matan ma wani     ɓangare na jikinsu na zubar da ruwa mai wari ko kuma kumburi na babu gaira    babu dalili.

Wannan kan sa miji ya tsani matarsa, idan kuma aka yi rashin sa a shi ma yaɗauki cutar, babu mamaki matarsa ba ɗaya bace dukkansu ya shafa musu wannan cuta ta sanyi.

Na san da yawan mata na sane da duk abinda na faɗa don ba komai na faɗa ba cikin illolin da sanyi kan haifarwa mace a lokuta da dama.

Idan kin kasance kina ɗauke da wannan cuta, ko kuma kina daar uwa da ke ɗauke da wannan cuta, ki   bata     labarin mujallar Matashiya domin a nan ne za mu fara kawo hanyoyin da za a bi don rabuwa da cutar bakiɗaya.

Da farko idan kina ɗauke da cutar sanyi, wanda bai yi yawa a jikinki ba za ki fara gwada waɗannan hanyoyin kamar haka.

Na farko a kullum da safe za ki samu ruwan ɗumi amma ba mai zafi sosai ba kuma ki tabbata ruwan mai kyau ne sosai da sosai abin da za ki zuba ma ki          tabbatar yana da tsafta    sosai, bayan kin zuba       ruwan zafin a cikin roba mai girma wadda za ki iya shiga ciki ki zauna, sai ki samu wajen mai kyau ko da banɗakin da za ki amfani da shi ma ki tabbatar yana da tsafta sosai kin san idan za a yi           maganin cuta sai an kaucewa duk wata hanya da za a iya samun wata cutar.

 

Za ki samu ruwan nan ki shiga ciki, ki ɗauki kamar minti 30 a ciki ba tare da kin tita ba.

Kash, lokaci ya cimmana a yanzu amma mu tara a fitowa ta gaba don ɗorawa daga inda muka tsaya.

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: