Masarautar Saudiya ta musanta cewa, Yarima mai jiran gadon sarautar kasar Muhammad Bin Salman, na shirye-shiryen sayen ƙungiyar Manchester United.
Bayanan baya bayan nan na nuni da cewa Muhammad Bin Salman zai sayi ƙungiyar manchester dake ƙasar ingila ya bayyana ne bayan taron da ya gudana tsakaninsa da wasu shugabannin kungiyar.
Sai dai ministan yaɗa labaran Saudiya Turki al-Shabanah, ya ce shugabanin Manchester United, sun tattauna da Yarima mai jiran gado ne kan batutuwan da suka danganci ɗaukar nauyin kungiyar a wasu fannoni.
jaridar Sun da ke Birtaniya, ta wallafa labarin Yarima Muhammad bin Salman, yayi tayin biyan dala biliyan 4 da miliyan 900, domin sayen kungiyar Manchester United.
Jaridar ta rawaito cewa tun a watan Oktoba na 2018 Yariman na Saudiya ya gabatar da tayin nasa.
Sai dai kamar yadda kukaji masarautar ta saudiya ta musanta wannan labari.


