Ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Nasssarawa a Jihar ano Muhammadu Aminu Adamu wanda ake kira Abba Boss ya jadda aniyarsa ta zaɓar jam’iyyar APC tun daga sama har ƙasa a zaɓen da muke tinkara.

Abba Boss wanda ya kasance jigon tafiyar kwankwasiyya a baya, yanzu dai ya ce ya yar da kwallon mangwaro ya huta da ƙuda ganin yadda ya ce tafiyar madugun ta tasamma zama shirirta.
Cikin shirin wata wata na Abokin tafiya da Mujallar Matashiya ke gabatarwa Abba Boss ya ce sun shiga jam’iyyar APC ne don kawo cigaba tare da sauya gurbin da aka samu naƙasu bisa kuskure, kuma za su yi duk mai yuwuwa wajen ganin sun ɗabbaƙa ayyukan da mutane suke buƙata kamar yadda suka faro.

Ya cigaba da cewar ko da zaman lafiya da aka samu ya isa ya zama misali na cewar gwamnatin APC ta gudanar da dukkan aikin da mutane suke so, sakamakon a baya zaman lafiyar ya yi ƙaranci.

“Bakin rai bakin fama Za mu marawa dukkan ɗan jam iyyar APC baya har su kai ga nasara don amfanawa al’umma, kuma ko a yanzu mun gama shirya tsarin da jama’a za su ji daɗi matuƙar suka sake amincewar jam iyyar komawa a karo na biyu” inji Abba Boss.
Ya ce ko da a ma auni za a ga bambancin ingantattun ƴan takararsu daban yake da na sauran jam iyya, domin na APC suna da nagarta, ba sa sata, kuma suna aiki tuƙuru.