Tare da Rabi u Sanusi Katsina
Ita dai Tarbiya ta samo asali ne daga tushen iyaye, Tarbiya tana ginuwa ne daga samun uwa tagari domin ita ke kasancewa makaranta ga ‘yayanta. Shiyasa Masoyina Annabi Muhammadu “Sallalahu Alaihi Wassalam” ya yi umurni da a auri mace ma’abociyar addini domin kasancewar saita san addini sannan tasan yadda zata yi ta tarbiyantar da ‘yayanta. A yau mun wayi gari tarbiyar matasanmu tana gurbacewa ta hanyoyi da dama a wannan zamani da muke ciki. Ana samun matsala daga manyan mutane misali, yan siyasa suna amfani da matasa a wannan lokaci, don haddasa gaba da kiyayya a tsakaninsu, da yin qokarin aiki da matasa wajen basu makamai don kashe musu abokan gabansu, wannan ba daidai bane. Ya kamata matasa mu yi wa kanmu fada kuma mu duba duk sanda aka umurce mu da kai hari na kisa ba zaka ga daya daga cikin ‘yayan wanda suka tura mu ta’addancin ba, saboda haka mai zai sa mu tsaya muna kashe junanmu?, bayan Allah yana cewa a cikin suratul Anfaal :-  (Fattakulla wa aslihu zata bainikum wa’adillaha warasulahu inkuntum mu’umineen).
Ma’ana:- (kuji tsoron Allah kuma ku daidaita tsakaninku kuma
kubi Allah da Manzonsa idan kun kasance muminai).
Kuma Allah ya kara da cewa acikin suratul Hujurat :- (Innamal mu’uminuna ikhwatun fa aslihu baina akawaikum wattaqullaha la’allakum turhamuun).
Ma’ana :- (Su muminai yan’uwan juna ne don haka idan wani abu ya faru, to ku daidaita tsakaninku kuma kuji tsoron Allah ko a jikanku) to saboda me matasa zamu ringa kashe junanmu.
 *Rawar da Matasa suka taka a baya.*
A baya dai matasa sun taka rawa sosai a sassa daban – daban na ci gaban Najeriya. Kusan za a iya cewa su ne kan gaba wajen tafiyar da al’amuran qasar bayan samun ‘yancin kanta.
Alal misali, shugabanni irin su Janar Murtala Muhammad da Janar Yakubu Gowon, sun shugabanci kasar suna matasa, duk da cewa dai shugabanci ne na soja, amma wasu na ganin sun taka rawar gani. Haka kuma ko a yanzu akwai mutane irin su kakakin Majalisar Wakilai ta qasa, wanda shi ma matashi ne. Sai dai wasu na ganin a yanzu matasan ba su da makoma mai kyau, ganin cewa ‘ya’yan wane da wane ne kawai ke iya samun damar yin ilimi mai inganci, saboda kusan baki xayan makarantun gwamnati ba sa tafiya yadda ya kamata. Wanda
haka yana xaya daga cikin abin da ya janyo mana rikicin Boko Haram a Kasar Mu Ta Gado, wanda muke ta addu’ar Ubangiji Allah ya kawo mana karshen sa Amin.
 Ubangiji Allah ka shirya mana Matasanmu, kasa su amfani al’umma Amin da Addinin mu Amin summa amin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: