Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta tabbatar da cewa ba gudu ba ja da baya zata gudanar da zaɓe A ranar Asabar 23-02-2019.

Shugaban hukumar Prof yakubu Mahmud ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya laraba.
Yakubu ya bayyana cewa tuni suka shawo kan matsalar da tasa suka ɗage zaɓen a makon da ya gabata don haka hukumar ta shirya tsaf don ganin an gudanar da zaɓe mai inganci a ƙasa baki ɗaya.

