Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Kai tsaye zaɓen 2019 a Najeriya , a jihar jigawa an nemi takardun zaɓe sama ko ƙasa an rasa

A ƙaramar hukumar Kiyawa jihar Jigawa a Najeriya, an nemi takardun zaɓe an rasa adai sai lokacin da ma aikatan zaɓe suka halarci mazaɓar shuwarin.

A zantawarmu da wasu daga cikin masu kaɗa ƙuri a sun bayyana mana cewar, sun halarci wajen zaɓen tun asuba amma har misalin ƙarfe biyu na rana ba a kawo akwatin zaɓe ba.

Wani da ya tabbatar mana da cewar an ɗauke curin takardun zaɓe guda biyar hakan ya sa ma aikatan zaɓen dakatar da aikin nasu har sai da suka koma ofishin hukumar zaɓe na ƙaramar hukumar.

Da yawan mutane sun fito don kaɗa ƙuri a sai dai babu jami an tsaro.

Wasu mutanen sun koka rashin wadatar kayan aiki kamar wajen dangwala ƙuri a da kuma ƙarancin taimako ga gajiyayyu da mata masu rauni.

  1. A nan ma matasa sun fito filin tamola don buga kwallon ƙafa yayin da ake gudanar da babban zaɓe a Najeriya.

asu matasa a Kano sun yanke shawarar fita titi don yin kwallon ƙafa sakamakon rashin samun katin zaɓensu na dindindin.

A ƙaramar hukumar fagge a najeriya matasa da yawa sun fito titi suna buga kwallon ƙafa a rashin samun katin zaɓensu na dindindin.

  1. 9

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: