Hukumar tsaron farin kaya sun yi ram da Buba Galadima ne bayan da suka yi masa dirar mikiya bayan ya fita daga gidansa.

Buba Galadima dai ya yi wasu kalai da ake tunanin sune suka haddasa kamashi.

“Bin shi aka yi ya na kan titi, aka cimmasa aka kama”, inji Kola tare da karin cewa su na ta kokarin neman samun karin haske.

Muryoyin ‘yan adawa na ci gaba da karajin cewa a gaggauta sakin Galadima ba tare da wani bata lokaci ba. Sannan kuma su na kyautata zaton cewa ya na hannun jami’an SSS a tsare.

Kakakin SSS ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba zai iya sanin an kama shi ko ba a kama shi ba.

Kama Buba Galadima ya biyo bayan wani kira da kakakin kamfen din Buhari, Festus Keyamo ya yi, inda ya nemi a gaggauta kama Galadima.

Keyamo ya yi zargin cewa Galadima ya fitar da wani bidiyo, inda ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Dama kuma tun kafin haka, PDP ta bayyana a yau Lahadi da rana cewa akwai kulle-kullen da gwamnati ke yi domin ta kama wasu manyan rikakkun masu adawa da ita.

Buba Galadima ya kasance a sahun gaba wajen sukar gwamnatin Buhari tun bayan raba hanya da suka yi shekarun baya kafin zaben 2015.

Akwai babbar ‘yar sa wadda a yanzu haka ta ke aiki a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja. Kuma a lokacin auren ta, Buhari ne uban amarya, shi ya bayar da auren ta, watau waliyyin ta kenan.