A ƙaramar hukumar Kiyawa jihar Jigawa a Najeriya, an nemi takardun zaɓe an rasa adai sai lokacin da ma aikatan zaɓe suka halarci mazaɓar shuwarin.

A zantawarmu da wasu daga cikin masu kaɗa ƙuri a sun bayyana mana cewar, sun halarci wajen zaɓen tun asuba amma har misalin ƙarfe biyu na rana ba a kawo akwatin zaɓe ba.
Wani da ya tabbatar mana da cewar an ɗauke curin takardun zaɓe guda biyar hakan ya sa ma aikatan zaɓen dakatar da aikin nasu har sai da suka koma ofishin hukumar zaɓe na ƙaramar hukumar.

