Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai Siyasa

Jami’an tsaro sun cafke Buba Galadima sakamakon faɗin sakamakon Zaɓen shugaban ƙasa

jami’an tsaro sun cafke na hannun daman ɗan takarar Shugaban najeriya na babbar jam’iyyar adawa ta PDP Buba Galadima, kamar yadda shugabancin jam’iyyar ta tabbatar.
har zuwa yanzu babu wani cikakken dalilin kama shi da aka yi, sai dai kakakin jam’iyyar PDP Kola
Ologbonyan, ya ce an kama shi ne a Abuja.
A wani rahoto ya tabbatar da cewa kakakin yaƙin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari, Festus Keyamo ne ya buƙaci da a kama Buba Galadima, wanda ya ce ya fitar da wani bidiyo, da a cikinsa ya ke bayyana cewa Atiku Abubakar shi ne ya lashe zaɓen shugabancin Najeriya, duk da cewa hukumar zaɓen kasar INEC ba ta bayyana sakamakon zaɓen ba.
Ƴan takara 73 ne ke fafatawa a matakin zaɓen kujerar shugabancin Najeriyar, sai dai takarar ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci Muhd Buhari da kuma ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne ta Najeriya

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: