Babbar jam iyyar mai adawa a Najeriya PDP ta yi fatali da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

Shugaban jam iyyar PDP na ƙasa Secundus Uche ne ya bayyana cewar suna da sakamakon zaɓe sahihi a hannunsu, don haka ba su gamsu da wanda ake gabatarwa a gaban shugaban zaɓe ba.
A yau litinin aka fara sauraron sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Najeriya wanda a halin yanzu APC ke kan gaba.

