Connect with us

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa, kai tsaye sakamakon jihar Zamfara

Published

on

Baturen zaɓe Farfesa Kabiru Bala

ANN 25

ADA 947

APC 438.682

APN 67

ASD 41

PDP 125.423

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Tarwatsa Sansanin Yan Boko Haram Da ISWAP

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar gano wani sansanin mayaƙa Boko Haram da ISWAP a dajin sambisa tare da lalatashi sannan su ka ƙwato makamai.

A wata sanarwa da rundunar ta sanar a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya, rundunar ta ce sun tarwatsa sansanin mayaƙan sannan sun lalata wasu makamai tare da ƙato wasu.

An kai harin ne Ngumne, Kawaran, Mangu duka a dazukan Sambisa da Tinbuktu a jihar Borno.

Rundunar ta yi amfani da makamai masu hatsari wajen tarwatsa sansanin sannan an ƙato manyan bindigu da hasashi da wasu makamai.

Ta ce hakan na daga cikin ayyukan da ta ke yin a kawar da dukkanin ayyukan ta’addanci da ake aikatawa a jihar.

Jihar Borno na fama da rikicin mayaƙan ISWAP da Boko Haram fiye da shekaru 10 da su ka gabata.

Continue Reading

Labarai

Sabuwar Bullar Annoba Ta Kashe Mutane 45 A Kano

Published

on

Aƙalla mutane 45 ne su ka rasa rayuwarsu bayan ɓullar wata annoba a Kano.

Mutane a ƙauyen Gundutse a ƙaramar hukumar Kura a Kano na jimamin rasuwar mutane 45 mafi yawa daga ciki mata ne da ƙananan yara bayan da wata annba ta ɓarke a ƙauyen.

Al’amarin ya faru ne bayan da mafi yawa daga cikinsu su ka nuna alamar kamuwa da zazzaɓin cizon sauro, mashaƙo da ama.

Al’ummar sun shida ɗimuwa bayan da ake rasa mutane biyar a kowacce rana.

Wani mazaunin garin mai suna Abu Sani ya shaida cewar, ya rasa ƴaƴansa gida biyu wanda ya yi tunanin ko zazzaɓin cizon sauro ne ya yi ajalinsu.

Wata mai suna Hajara Abubakar ta ce zuwa yanzu ta san mutane 40 da su ka mutu a sakamakon annobar.

Yahaya Tijjani Kura da ke zama shugaban riƙo na ƙaramar hukumar, ya tabbatar da faruwar hakan sai dai y ace zuwa yanu mutane uku ne su ka mutu.

Yayin dama’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce bat a da masaniya dangane da faruwar lamarin zuwa yanzu, domin bas u samu sanarwa a hukumance daga ƙaramar hukumar ba, sai dai ana gudanar da bincike a kai.

Continue Reading

Labarai

Published

on

Babbar kotun jihar Kano ta tabbatar da matakin dakatar da tsohon gwamnan Kano daga jam’iyyar APC tare da hanashi bayyana kansa a matsayin shugabanta ana]l ƙasa

Mau buƙata ta musamman sun koka a kan yadda ake samun ƙaruwar mabarata daga cikinsu

Ɓullar wata nnoba a Kano ta yi sanadiyyar rasa rayuwar mutane 45

Kotu a Kogi ta dakatar da hukumar EFCC daga  kama tsohon gwamnan jihar Yahaya Bello

Sojojin Najeriya sun bankaɗo wata maɓoyar Boko Haram tare da tarwatsata a jihar Borno

Laraba

8 Sahwwal 1445

17 4 2024

Babbar kotun jihar Kano ta tabatar da dakatarwar da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Ganduje su ka yi wa tsohon gwamnan Kano Dakta Abdullahi umar Ganduje.

Ƙarar da Laminu Sani da Haladu Gwanjo su ka shigar gaban kotun, sun jaddada matsayarsu na dakatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ɗan jam’iyyar daga mazaɓarsa ta Ganduje.

Tun a ranar Litinin aka wayi gari da labarin wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwar jam’iyyar a mazaɓar Ganduje, das u ka sanar da dakatar da tsohon gwamnan daga cikin jam’iyar.

Sai dai daga bisani shugaban jam’iyyar a matakin mazaɓa da shugaban majalisar na ƙaramar hukumar Dawakin Topa da ma shugabancin jam’iyyar a matakin jiha sun yi watsi da batun.

Jam’iyyar ta zargi mutane biyun das u ka shigar da ƙarar da cin amanar jam’iyyar, ta hanyar yi wa jam’iyyar adawa aiki kamar yadda shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar Dawakin Topa ya shaida.

A hukuncin da mai shari’a Usman Malam Na’abba ya yanke a ranar Talata, ya tabatar da matakin da mambobin biyu daga cikin tara su ka ɗauka na dakatar da Ganduje daga cikin jam’iyyar.

Bayan faruwar haka, jamiyyar APC ta zargi abokiyar hamayyarta ta NNPP da hannu a lamarin das u ka kira maƙarƙashiyar.

Sai dai tuni jam’iyyar NNPP ta nesanta kanta da hannu a ciki, wada ta ce lamari ne da ya shafi jam’iyyar APC kuma abu ne na cikin gida babu hannunsu a ciki.

Abdullahi Ganduje shi ne shugaban jam’iyyar APC a ƙasa.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Ganduje ya ce sam bai girgiza ba kuma har yanzu ya na nan dara matsayin shugaban jamiyyar na ƙasa.

A wani bidiyo da ya  ke yawo a kafofin sa da zumunta, Ganduje ya zargi gwamnatin Kano da jam’iyyar NNPP da hannu a abinda ya kira maƙarƙashiya da aka yi masa kan batun dakatar da shi daga cikin jam’iyyar daga matakin mazaɓa.

Ganduje ya ce ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kuma ya tabbatar masa da cewar har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC.

Wannan na zuwa ne bayan da wani ɓangare na shugabancin  jam’iyyar a mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawain Tofa su ka sanar da dakatar da shi daga cikin jam’iyyar.

Sai dai a wani bidiyo da aka gano shugaban jam’iyyar na mazaɓar y ace ba da aywunsu wannan sanarwa ta fita ba, kuma waɗanda su a fitar da sanarwa ba sa tare da su.

An fara wanan sa toka sa katsin ne tun bayan da kotun ƙoli ta tabbatar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan Kano.

A ƴan kwanaki nan dai gwamnatin Kano ta shugar da ƙara a gaban kotu wanda take zargin tsohon gwamnan Abdullahi ganduje da yin almundahana, aiwatar da gwamnati  a yadda ya kamata ba.

Ƙungiyar masu buƙata ta musamman ta arewacin Najeriya ta koka a kan yadda ake sake mayar da su baya duk da cewar an zaɓo ɗan cikinsu tare da bashi muƙami a fadar shugaban ƙasa.

Yarima Sulaiman Ibrahim shugaban ƙungiyar na arewa, shi ne ya bayyana haka yayin ganawa da Matashiya TV yau Laraba.

Abba Isah shi ne mashawacin shugaban ƙasa a kan masu buƙata ta musamman wanda aka zaɓo daga jihar Yobe.

Ya ce dun da an zaɓo ɗan cikinsu kuma aka masa mashawarcin shugaban ƙsa kan masu buƙata ta musamman, bay a yin abinda ya kamata.

Y ace maimakon ya mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga masu buƙata ta musamman, sai ya fi karkata wajen raba abinda bai kai ya kawo ba.

A sakamakon haka y ace ba za su lamunta ba domin a wannan lokaci ana samun ƙaruwar mabarata daga cikinsu maimakon raguwarsu.

A don haka su ka yi koka domin a cewarsu, ba ya yin abinda ya kamata wajen sauke nauyin da ke wuyansa.

Za ku samu cikakkiyar tattaunawar a shafukanmu na YouTube da Facebook.

Break

Aƙalla mutane 45 ne su ka rasa rayuwarsu bayan ɓullar wata annoba a Kano.

Mutane a ƙauyen Gundutse a ƙaramar hukumar Kura a Kano na jimamin rasuwar mutane 45 mafi yawa daga ciki mata ne da ƙananan yara bayan da wata annba ta ɓarke a ƙauyen.

Al’amarin ya faru ne bayan da mafi yawa daga cikinsu su ka nuna alamar kamuwa da zazzaɓin cizon sauro, mashaƙo da ama.

Al’ummar sun shida ɗimuwa bayan da ake rasa mutane biyar a kowacce rana.

Wani mazaunin garin mai suna Abu Sani ya shaida cewar, ya rasa ƴaƴansa gida biyu wanda ya yi tunanin ko zazzaɓin cizon sauro ne ya yi ajalinsu.

Wata mai suna Hajara Abubakar ta ce zuwa yanzu ta san mutane 40 da su ka mutu a sakamakon annobar.

Yahaya Tijjani Kura da ke zama shugaban riƙo na ƙaramar hukumar, ya tabbatar da faruwar hakan sai dai y ace zuwa yanu mutane uku ne su ka mutu.

Yayin dama’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce bat a da masaniya dangane da faruwar lamarin zuwa yanzu, domin bas u samu sanarwa a hukumance daga ƙaramar hukumar ba, sai dai ana gudanar da bincike a kai.

Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar gano wani sansanin mayaƙa Boko Haram da ISWAP a dajin sambisa tare da lalatashi sannan su ka ƙwato makamai.

A wata sanarwa da rundunar ta sanar a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya, rundunar ta ce sun tarwatsa sansanin mayaƙan sannan sun lalata wasu makamai tare da ƙato wasu.

An kai harin ne Ngumne, Kawaran, Mangu duka a dazukan Sambisa da Tinbuktu a jihar Borno.

Rundunar ta yi amfani da makamai masu hatsari wajen tarwatsa sansanin sannan an ƙato manyan bindigu da hasashi da wasu makamai.

Ta ce hakan na daga cikin ayyukan da ta ke yin a kawar da dukkanin ayyukan ta’addanci da ake aikatawa a jihar.

Jihar Borno na fama da rikicin mayaƙan ISWAP da Boko Haram fiye da shekaru 10 da su ka gabata.

Babbar kotun jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja ta dakatar da hukumar hana cin hanci da rashawa EFCC kamawa, tsarewa tare da gurfanar da tsohon gwamnan jihar Yahaya Bello.

Umarnin kotun wanda ta yanke a yau Laraba, ta hana hukumar kama tsohon gwamnan har said a izinin kotu.

Alƙalin kotun Justice I.A Jamil ne ya karanto hukuncin byan da hukumar ta matsa don ganin ta kama tsohon gwamnan.

Ana zargin tsohon gwamnan da yin sama da faɗi da wasu kuɗaɗen jihar a lokacin da ya na gwamna.

Kotun ta soke umarnin wata kotu a jihar da ta bai wa hukumar dammar kama tsohon gwamnan.

A yau Laraba ne hukumar ta kai sumame don kama tsohon gwamnan a gidansa da ke Abua, sai dai daga bisani ya tsallake kamun wanda aka tseratar da shi.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: