Shugaba Muhammadu Buhari ya kasance mutumin da talakawa suke ƙauna har zuciyarsu, bisa yadda tsarin mulkinnsa na kare dukiyar al’umma.

A cikin mulkina na farko ya samar da ayyukan raya ƙasa kamar Tituna a wasu yankin, da samar da tsaro, duk da cewa wasu na ganin ya yi burus da wasu yankunan.

Cin hanci da rashawa shi ne abin da gwamnatin shugaba Buhari ke mayar da hankali wajen ganin an cafke duk wani da aka samu da badaƙalar.

Muhammadu Buhari shi ne shugaban da ya kafa tarihi, mutumin da ya fito da farin jinin talakawa, har ma ta kai mutane sun tura kuɗaɗensu don hidimta masa a lokacin takararsa ta farko.

A lokacin Mulkin shugaba Buhari Mujallar Matashiya ta kyallo wasu ayyuka da ya shimfiɗa ciki kuwa har da ƙoƙarin samawa matasa aikin yi ta hanyar N-POWER.

Inda kuma mabiyinda kuma abokin karawarsa na jam iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya ke binsa a yawan ƙuri u.

Muhammadu Buhari ya samu nasara a karo na biyu bayan da ya lashe zaɓen kujerar shugabancin ƙasar Najeriya a shekarar 2015

Muhammadu Buhari ya nemi takarar shugabancin ƙasar tun a ashekarar 2003 wanda bai samu nasara ba, hakan ya sa shi sake fitowa a shekarar 2007 haka zalika a lokacin abokin karawarsa Marigayi Umaru Musa Ƴar Adua ya samu nasara.

Hakan dai Muhammadu Buhari ya sake fitowa tarar shugabancin ƙasar a shekarar 2011 hakan dai a lokacin ma bai samu nasara ba sai a shekarar 2015 wandaya ci zaɓen tare da mataimakinsa Farfesa Ymi Osibajo.

Bayan zaɓen da aka gudanar a dukkan sassa na ƙasar Najeriya a ranar Asabar,  Shugaba Muhammadu Buhari ya shi ne ɗan takara da yake da mafi rinjayen ƙuri u.

Haka kuma Muhammadu Buhari ya kasance mutumin da ya mutane suka aminta da gaskiyarsa da riƙon amana kamar yadda ya ke faɗa a yayin yaƙin neman zaɓensa.

Mujallar Matashiya ta bankaɗo wasu kalamai da shugabanke yi yayin da ya je yaƙin neman zaɓe a wurare da dama, Buhari na bayyana cewar gwamnatinsu za ta inganta harkokin noma da kiwo, samar da tsaro, buƙasa tattalin arziƙi da kuma walwalar jin daɗin ƴan ƙasa.

Za mu ci gaba idan halin ya yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: