Hukumar dake kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa ta (NBC) taci tarar wasu kafafen yaɗa labarai bisa karya dokar hukumar.
Darakatan yaɗa labarai na hukumar ne malam ishaq Modibbo kawu ne, ya bayyana hakan ga manema labarai, inda yace ya zama wajibi su biya hukumar a tsakanin mako biyu kuɗaɗen da aka ci tarar su saboda.
Dokar da suka karya ya haɗa da yaɗa labaran siyasa a dai dai lokacin da hukumar ta ƙayyade lokacin da ta ware kafin zaɓe.
An ci tarar kafafen yaɗa labaran naira 500,000, wanda suka haɗa da NTA, AIT, TVC da channels TV.


