Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wa’adin mulkinsa na biyu zai kasance mai tsauri sakamakon irin alkawuran da ya dauka zai cika wa ‘yan Najeriya na habaka tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da tsaro.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da ministocinsa a lokacin da suka kawo masa ziyara a fadar shugaban kasar domin taya shi murnar lashe zaben kasar.
BBC Hausa ta rawaito cewa Shugaban ya ce ” Ina ganin shekaru hudu nawa na karshe a kan mulki za su zama tsaurara saboda ina tunanin mutane na da mantuwa, wannan ne ya sa duk wurin da naje ina kara tuni da cewa yakin neman zabenmu muna yin sa ne kan abubuwa uku.”

Shugaban ya bayyana tabbatar da tsaro a matsayin abu na farko inda ya ce sai an samar da tsaro kafin a iya mulkar kasa yadda ya kamata.

Ya kuma bayyana tattalin arziki a matsayin abu na biyu inda ya ce ”marasa aikin yi a Najeriya su ne babbar matsalar kasar, ya ce sama da kashi 60 cikin 100 na ‘yan kasar matasa ne wanda hakan na nufin ‘yan kasa da
Shugaban ya kara da cewa ”na ga alamun cewa Allah ya amsa addu’ar mu domin damina biyu da suka gabata Allah ya sa masu albarka wanda kafin hakan ne muka yi zurfin tunani muka sa ma’aikatar ayyukan gona da raya karkara tare da hadin gwiwar babban bankin Najeriya suka bayar da bashi ga manoma domin ganin cewa masu jini a jika da suke da gonaki sun koma gona.”
Shugaban wanda ya kuma tattauna a kan fitarsa yakin neman zabe ya ce hakan ya baiwa ‘yan adawa kunya da suke cewa bai da kuzarin mulkar Najeriya, amma ya ce wannan alama ce da ta nuna cewa ya shirya tsaf domin mulkar Najeriya na shekaru hudu masu zuwa.
A ranar Laraba ne dai hukumar zabe a Najeriyar ta bayyana Shugaban Kasar Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a ranar Asabar bayan ya fafata da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.
Sai dai dan takarar PDP Atiku ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zaben ta bayyana inda yake zargin an tafka kura-kurai wajen gudanar da zaben.