Ƙananan yara ne mafi yawa daga cikin ɗaliban da aka yi garkuwa da su

[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]
Daga Abdurrahman Abubakar Sada

‘Yan Bindiga/Masu Garkuwa da Mutane, sun yi awon gaba da wani gungun yara/matasa, a garin Shinkafi da ke jihar Zamfaran Najeriya.

A wata Makarantar Islamiyya da ke gidan Wanzamai (‘Yar’adua Tsohuwa), inda yaran ke karatu.
Jihar Zamfara dai ta dade cikin wannan musiba ta garkuwa da mutane.
Akalla a yanzu kullum sai mun wayi gari da irin wannan mummunan labarin (ko mai kama da shi), musamman Karamar Karamar Hukumar Shinkafi, wanda wannan Karamar Hukuma na daga cikin yankin da wannan matsala ta fantsama a fadin jihar. Cewar wani mazaunin garin Shinkafi.
Daga mafi munin hare-hare, ko a makon jiya, an samu wasu gungun ‘yan ta’adda sun bulla, inda suka kashe adadin mutane sama da talatin (ta yadda suka tare hanya da harbin matafiyan, ta bangaren Kauyen Atarawa har zuwa Kursasa, duka dai a Karamar Hukumar ta Shinkafi.