Wasu fursunoni 17 ne da ke ɗaure a gidan yarin Kaduna suka samu nasarar samun damar karatu a jami’ar tafi da gidanka ta Nijeriya wato (NOUN) yau Talata
a Kaduna.
Shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Adamu, ne ya bayyana hakan a daidai lokacin da akayi bikin maraba da sabbin ɗalibai da aka gabatar a gidan yarin Kaduna, dake kan hanyar Independence a garin Kaduna.
Abdullahi yayi kira tare da shawarartar sabbin ɗaliban da su yi amfani da wannan damar domin su zama ƴan kasa na gari, saboda a cewar shi wannan ba ƙaramar dama jami’ar ta basu ba, wacce in suka yi amfani da ita yadda ya dace zasu kasance ƴan kasa masu amfani bayan wa’adin su na gidan yari ya ƙare.
Fursononin sun samu damar karatun ne a fannonin ilimi daban-daban, da suka haɗa da tsangayoyin kimiya da fasaha, na ilimi, na karatun lauya da ilimin kimiyar aikin noma, 14 daga cikin daliban zasu fara digirin farko ne, sai uku daga cikinsu kuma karatun digiri na biyu.
Wannan ba ƙaramin dama ce fursunoni suka samu ba don gudanar da ilimi a lokacin da suke tsare a gidan yari.


